Tashin hankali: Bidiyon yadda Baban Chinedu ya dinga tona asirin babban abokinshi Rarara

Tashin hankali: Bidiyon yadda Baban Chinedu ya dinga tona asirin babban abokinshi Rarara

- Fitaccen jarumin barkwancin nan na masana'antar Kannywood ya fito ya bayyanawa wani sirri dake boye na Rarara da shugaban hukumar tace fina-finan Hausa

- Jarumin ya bayyana cewa yanzu babu abinda shugaban hukumar ta ce fina-finan ke yi sai aikin mawakin siyasa Rarara

- Ya bayyana cewa shugaban hukumar fina-finan ya san shi sosai ba sanin shanu ba, saboda haka shi yafi karfinshi iskancinsa sai dai ya yiwa wasu ba shi ba

A cigaba da kace nace da ake ta faman yi a masana'antar fina-finan Hausa ta Kannywood, sanadiyyar kama babban darakta Sunusi Oscar 442, bisa zarginsa da ake yi da fitar da wani bidiyo ba bisa ka'ida ba.

Yanzu haka shima fitaccen jarumin barkwancin nan da aka fi sani da Baban Chinedu ya fito yayi magana akan hukumar tace fina-finan Hausan, inda ya nuna irin munafurcin da shugaban hukumar tace fina finan suke hadawa da fitaccen mawakin nan Dauda Kahutu Rarara.

KU KARANTA: Tirkashi: Idan na cika shekara 40, zan auri maza 3, na gina musu gidaje sai na dinga zabar wanda zan kwanta da shi a cikinsu - Toyin Lawani

Ga abinda jarumin ya ce a cikin wani bidiyo da ya saki:

"Hukumar ta ce fina-finai ta jihar Kano, lamarinku yana bani dariya, Afakallahu ka san na sanka sosai, idan ma zaka yiwa wasu mu dai munfi karfinka mun saka ciki da waje.

"Yanzu kai aikin da kake yi shine aikin Rarara, idan Rarara yana fada da mutum da ya nuna shi sai ka kama shi ko kuma ka rike mishi fim, kamar yadda kuka yiwa Abdul Amat, a fim din shi saboda yana da matsala da Rarara, kuka rike fim din kuka ki saki, tun fim ana taya shi miliyan uku da rabi sai da ya dawo dubu dari shida kuka saki, bai yi muku laifin komai ba, saboda kawai ku karya mishi jari.

"Haka Sunusi Oscar, yanzu yaje ya gama hada wakokinsa na APC, duk da dai ku APC na ku iya Kano ne kawai, dama a sama ungulu da kan zabuwa kuke yi, yaje ya gama aikin wakokinsa ya dawo, saboda kawai ba kwa yin shiri dashi kun tura anje an kama shi."

Ga bidiyon a kasa:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel