Sunaye da mukami: Buhari ya yi wasu sabbin muhimman nade-nade 8 a ofishin Osinbajo

Sunaye da mukami: Buhari ya yi wasu sabbin muhimman nade-nade 8 a ofishin Osinbajo

Shugaban Kasa Muhammaduu Buhari ya amince da sake nadin Ade Ipaye a matsayin mataimakin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa. Mr Ipaye tsohon Attorney Janar ne kuma kwamishinan Shari'a a jihar Legas da ke aiki daga ofishin mataimakin shugaban kasa.

Shugaban kasar ya kuma amince da sake nadin Adeyemi Dipeolu, a matsayin Mai bayar da shawara na musamman ga shugaban kasa kan Harkokin Tattalin Arziki; Da kuma Maryam Uwais da za ta cigaba da rike mukaminta a matsayin mai bayar da shawara na musamman kan Ayyukan Rage Talauci da kuma Babafemi Ojudu a matsayin mai bayar da shawara na musamman kan Harkokin Siyasa.

DUBA WANNAN: Ba ni da wani ilimi a kan ma'aikatan da aka bani in rike - Sabon ministan Buhari

Sauran da ake sake sabunta nadinsu sun hada da Jumoke Oduwole da za ta rika bawa shugaban kasa shawara kan saukaka yin kasuwanci.

Kazalika, Shugaban kasa ya kuma nada Ahmed Rufai Zakari a matsayin mai bayar da shawara na musamman kan Gine-Gine, Obafela Bank-Olemoh, babban mai bayar da shawara kan Tallafin Ilimi, Louis Odion a matsayin babban mataimaki kan Jaridu da Ajuri Ngelale a matsayin babban mai bayar da shawara kan Harkokin da suka shafi Al'umma.

Dukkan wadanda aka yi wa naddin za suyi aiki ne a ofishin mataimakin shugaban kasa.

Baya ga Zakari, Bank-Olemoh, Odion da Ngelale, dukkan sauran wadanda aka sabbunta nadinsu wa'adinsu ya fara ne tun ranar 29 ga watan Mayun 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel