Dalilin da ya sa muka kara yawan ministoci - Buhari

Dalilin da ya sa muka kara yawan ministoci - Buhari

Kamar yadda muka sani a yau Laraba, 21 ga watan Agusta ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da sabbin ministocinsa na Next Level, inda a hakan ne aka samu karin ma’aikatu bayan an sanar da aikin da kowani minista zai kama.

A farkon mulkin Shugaban kasar, ya hade wasu ma’aikatu yayin da ya raba wasu da-dama. Wannan karo kuma an yi akasin haka inda har ta kai an kirkiro wani sabon ofis.

Sai dai kuma Shugaba Buhari ya bayyana cewa sun kara yawan ministoci ne "saboda arzikin kasar ya karu".

Kakakin Shugaban kasar, Mallam Garba Shehu ne ya bayyana hakan a wata hira ta musamman da ya yi da manema labarai jim kadan bayan kammala bikin rantsuwar.

Sabbin ma’aikatun dai sun hada da: Ma'aikatar Jin-kai da Walwalar 'Yan kasa wacce Sadiya Umar farouk za ta jagoranta, sai kuma Ma'aikatar Harkokin 'Yan Sanda wacce Mohammed Maigari Dangadi zai jagoranta.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya kafa ma’aikatar bada agaji, ya maido da wasu tsofaffin Ma’aikatu

Garba Shehu ya ce a karon farko Shugaba Buhari ya rage ministocin ne saboda su dace da aljihun gwamnati.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel