An haramta ayyukan kungiyoyin yan kato da gora a jahar Kaduna

An haramta ayyukan kungiyoyin yan kato da gora a jahar Kaduna

Rundunar Yansandan Najeriya, reshen jahar Kaduna ta sanar da haramta ayyukan kungiyoyin matasa yan sa kai, wadanda aka fi sani da suna ‘yan kato da gora’, kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya ta bayyana.

Rundunar ta sanar da haramta ayyukan kungiyoyin ne ta bakin kaakakinta, DSP Yakubu Sabo cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Laraba, 21 ga watan Agusta, inji majiyar Legit.ng.

KU KARANTA: Hukumar DSS ta bankado wasu mutane 2 dake kokarin kawar da gwamnatin Buhari

Kaakaki DSP Sabo ya bayyana cewa rundunar Yansanda tana gargadi kada wani ya sake bayyana kansa a matsayin dan kato da gora, balle kuma ya aikata wani aiki da sunan tsaro a gaba daya jahar Kaduna.

Kaakakin ya cigaba da cewa duk wanda hukumar Yansanda ta kama ya karya wannan umarni zai gamu da fushin hukuma, kuma za’a yi amfani da duk hanyoyin da doka ta tanadar don hukuntashi, ko wanene.

“Don haka rundunar Yansandan jahar Kaduna take neman hadin kai da goyon bayan jama’a ta wajen bata muhimman bayanai game da ayyukan miyagu a unguwanninsu domin rundunar ta samu daman karesu yadda ya kamata.” Inji shi.

Sai dai wasu mazauna garin Kaduna suna bayyana rashin jin dadinsu da wannan doka, inda suka nuna muhimmancin yan kato da gora sakamakon sune mafi kusa da jama'a, kuma suke kai musu dauki cikin gaggawa.

A wani labarin kuma, Wasu gungun yan bindiga sun kaddamar da mummunan hari a wasu kauyuka guda uku a jahar Katsina a daren Lahadi, 18 ga watan Agusta, inda suka kashe mutane 17.

Baya ga mutane 17 da suka mutu, akwai wasu mutane da dama da suka samu munanan rauni a sanadiyyar wannan hari da yan bindigan da suka kai, sa’annan sun yi awon gaba da wasu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel