Buhari ya sakanka ma jama’an Arewa da manyan mukaman ministoci 14
Biyo bayan rantsar da sabbin ministoci da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a ranar Laraba, 21 ga watan Agusta, a iya cewa shugaban kasa ya saurari koken jama’an Arewa, kuma ya share musu hawaye.
Wani bincike da Legit.ng ta gudanar ta hanyar nazari a kan mukaman da shugaban kasa ya baiwa sabbin ministocinsa, yar nune ta nuna shugaba Buhari ya kula da matsalolin yan Arewa, inda ya basu manyan ma’aikatu wadanda suke da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin kasa.
KU KARANTA: Hukumar DSS ta bankado wasu mutane 2 dake kokarin kawar da gwamnatin Buhari
Da farko dai shugaban kasa Buhari ya cigaba da rike mukaminsa na babban ministan man fetir, yayin da ya baiwa sabbin ministoci daga jahohin Arewa maso yammacin Najeriya mukamin manyan ministoci ba kanana ba, kamar haka:
1- Suleiman Adamu – Jigawa, ma’aikatan ruwan
2- Zainab Shamsuna Ahmed – Kaduna, ma’aikatan kudi, kasafin kudi da tsare tsare
3- Dr. Mohammad Mahmoud – Kaduna, ma’aikatan muhalli
4- Mohammed Sabo Nanono – Kano, ma’aikatan noma
5- Maj. Gen. Bashir Magashi (rtd) - Kano, ma’aikatan tsaro
6- Hadi Sirika – Katsina, ma’aikatan sufurin jirgin sama
7- Abubakar Malami – Kebbi, ma’aikatan shari’a
8- Mohammed Maigari Dangyadi – Sokoto, ma’aikatan kula da Yansanda
9- Sadiya Umar Faruk – Zamfara, ma’aikatan jin kai, kula da yan hudun hijira da cigaban jama’a
Haka zalika akwai sauran manyan ma’aikata da shugaban kasa Buhari ya aika da jama’an Arewa da suka hada da:
10- Lai Mohammed – Kwara, ma’aikatan watsa labaru
11- Engr. Sale Mamman – Taraba, ma’aikatan lantarki
12- Muhammed Musa Bello – Adamawa, babban birnin tarayya Abuja
13- Adamu Adamu – Bauchi, ma’aikatan ilimi
14) Ali Isa Pantami – Gombe, ma’aikatan sadarwa
Daga karshe akwai wasu kananan ma’aikatu guda 7 da Buhari ya sake nada mutanen Arewa a matsayin kananan ministoci da suka hada da:
1) Abubakar D. Aliyu – Yobe, ma’aikatan ayyyka da gidaje
2) Ramatu Tijani Aliyu – Kogi, ma’aikatan babban birnin tarayya Abuja
3) Gbemisola Saraki – Kwara, ma’aikatan sufuri
4) Amb Maryam Katagum – Bauchi, ma’aikatan kasuwanci da zuba jari
5) Mustapha Baba Shehuri – Borno, ma’aikatan noma
6) Mohammed A. Abdullahi – Nasarawa, ma’aikatan kimiyya da fasaha
7) Amb. Zubairu Dada – Niger, ma’aikatan harkokin waje
A jimlace mutanen Arewa 21 ne suka samu maukamai a cikin sabbin ministocin Buhari
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng