To fah: 'Yammatan yanzu duk 'yan iska ne, samari a lura da kyau kafin aje ayi zaben tumun dare - Jaruma ta shawarci samari

To fah: 'Yammatan yanzu duk 'yan iska ne, samari a lura da kyau kafin aje ayi zaben tumun dare - Jaruma ta shawarci samari

- Fitacciyar jarumar Nollywood Uche Elendu ta shawarci maza da su lura da kyau wajen zabar matar da zasu aura domin matan yanzu basu da hali mai kyau

- Ta kuma bayyana yadda mata da yawa suke kokari sosai wajen ganin aurensu ya dore a gidan mazajensu

- Haka kuma ta bayar da shawara akan irin hanyoyin da mazaje zasu dinga bi domin ganin aurensu ya dore da matayensu

Fitacciyar jarumar Nollywood kuma mai shirya fina-finai, Uche Elendu ta shawarci samari kada suyi gaggawar aure a wannan lokacin, ganin yadda mata na gari suke wahala.

Uche Elendu ta bayyana cewa abinda mata da yawa suka fi so shine, mutumin da zai kula dasu ya nuna musu soyayya da kuma wanda zai tsaya ya sauraresu ya fahimce su. Ta kara da cewa mata da yawa suna kokari sosai wajen ganin sun kare martabarsu a gidan aure wajen ganin aurensu bai samu matsala ba, kuma abin yana yi musu ciwo sosai idan aka dora musu laifi bayan sun rabu da mazajensu.

KU KARANTA: Kullu Nafsin Za'ikatul Maut: Amarya da Ango sun mutu a cikin daren amarcinsu

Ga abinda ta ce:

"Mata na gari wahala suke a wannan lokacin, idan ka samu kada ka sake kayi wasa da ita, ko kuma kaje ka dinga tunanin zaka samu wacce ta fita, ba zama lallai ka dace ba. Ba kowacce mace bace take da son abin duniya, da yawa daga cikinmu muna son mutum mai kulawa, soyayya da kuma fahimta, sauran abubuwa kuwa duk wannan ba damuwa bane indai namiji yana da wadancan.

"Mata da yawa suna yin iya bakin kokarinsu domin suga sun zauna a gidan mazajensu, kuma abin yana damunsu sosai idan auren ya mutu aka dora laifin a kansu.

"Dan Allah maza ku dinga kokari kuna nuna godiya da irin matar da kuka samu, ba sai kun takura kanku ba, kawai ka nuna mata matsayinka a rayuwa, ka dinga yawan sanyata dariya, kada ku bari sai wani can daga wani waje ya zo ya kwace muku mace wacce kuke ganin bata da amfani a wajenku."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel