Tirkashi: Ta kone gidan saurayinta kurmus saboda yaki yadda ya dinga kwanciya da ita kamar yadda suka yi alkawari

Tirkashi: Ta kone gidan saurayinta kurmus saboda yaki yadda ya dinga kwanciya da ita kamar yadda suka yi alkawari

- Wata mata ta kone gidan wani saurayinta da ya kirata gidanshi domin su kwana tare, bayan yaki amincewa ya kwanta da ita

- Matar mai suna Tajia Russell ta kone gidan kurmus inda shi kanshi mai gidan dakyar ya sha ta hanyar fitowa ta taga

- Yanzu haka dai jami'an hukumar 'yan sandan New Jersey sun cafke matar bayan sun gano wata shaida a kyamara dake nuna cewar matar na da hannu a lamarin

Jami'an hukumar 'yan sandan birnin New Jersy dake kasar Amurka sun kama wata mai suna Tajia Russell da laifin kone gidan saurayinta, saboda yaki yadda ya kwanta da ita kamar yadda suka yi alkawari.

Da yake bayani akan yadda lamarin yake, saurayin ya bayyana cewa ya gayyato budurwar tashi gidanshi, amma kawai sai ya tashi da misalin karfe hudu na dare ya tarar da gidansa ya dumame da hayaki, inda shima da kyar ya sha ta hanyar karya tagar gidan.

KU KARANTA: Farawa da Bismillah: 'Yammata 15 sun amsa tayin Adam A Zango na fitowa a sabon fim din sa saura 15 a fara tantancewa

Jami'an 'yan sanda sun zargi budurwar da aikawa saurayin wasu sakonni na zagi tare da kuma yi masa barazanar kisa.

Ga kadan daga cikin sakonnin da ta aika masa a kasa:

"Kasa na kashe kudin wajen zuwa wajenka, naga kana son mutuwa, kuma na rantse da Allah zan so ganin ka mutu."

Haka kuma kyamara ta dauki hoton Russell lokacin da take siyan ashana da fetur a wajen sayarda fetur kusa da gidan saurayin nata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel