Arziki: Salah ya nuna motocinsa masu tsada, har da ta naira biliyan 70

Arziki: Salah ya nuna motocinsa masu tsada, har da ta naira biliyan 70

- Mohamed Salah ya jefa kwallonsa ta farko a gasar Firimiya lig ta bana a wasar da suka buga da Norwich City

- Fitaccen dan kwalon kafar ya saya motar alfarma kirar Bentley Continental da kudin ta ya kai fam 160,000,000 domin murnar cin kwallon da ya yi

- Salah kuma yana da wasu motoccin alfarma da suka hada da Lamborgini, Mercedes Benz da wasu motoccin

Tauraruwar fittacen dan kwasan gaba na gefe na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Mohammed Salah tana ta haskawa tun bayan da ya komo kungiyar a shekarar 2017.

Zakaran na dan kasar Masar ya lashe kyautan golden boot sai biyu a jere bayan ya jefa kwalaye 22 a karshen kakar wasa ta 2018/2019.

Ya kuma taka muhimmiyar rawa wurin nasarar kungiyarsa yayin da suka lashe kofin gasar zakaru wato Champions League bayan sun lallasa Tottenham Hotspur 2 - 0 a wasar karshe.

Baya ga bajinta na jefa kwallaye a raga, dan kwallon kuma yana sha'awar sayan motoccin alfarma masu tsada da suka hada da Bentley, Lamborghini da Mercedes da aka gano a garejinsa.

DUBA WANNAN: Sabon salo: Wadanda suka yi garkuwa da dan limami sun karbi giya a madadin kudin fansa

Salah ya saya Bentley Continental GT Machine da aka kiyasta kudin ta kan fam 160,000 (N70,604,016,062.3017) don murnar kwallonsa ta farko da ya jefa a ragar Norwich City.

Kazalika, dan wasan yana da Lamborghini Aventador da kudinta ya kai fam 271,000 da Marsandi masu tsada guda biyu.

Marsandinsa ta farko, (Mercedes AMG Gle Coupe SUV) kudinta ya kai fam 65,000 yayin da ta biyun Mercedes-Benz SLS AMG Roadster kudinta ya kai fam 176,000.

Dan wasan kuma yana da Lamborghini Huracan ta kudinta ya kai fam 240,000 da Audi Q7 SUV da aka kiyasta kudin ta fam 54,000 yayin da motarsa da ta fi araha itace Toyota Camry da kudinta ya kai fam 29,000.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel