Sunaye: Jam'iyyar APC ta maye gurbin shugabaninta 3 da ta dakatar a Adamawa

Sunaye: Jam'iyyar APC ta maye gurbin shugabaninta 3 da ta dakatar a Adamawa

- Jam'iyyar APC ta zabi mutane uku da za su maye gurbin shugabaninta uku da ta dakatar a makon da ya gabata saboda samunsa da laifin yi wa jam'iyya zagon kasa

- Shugabanin da aka dakatar sune ne Alhaji Babangida Talase, Alhaji Saidu Naira da kuma Alhaji Aliyu Bakari

- An maye gurbinsu da wasu shugbanin jam'iyyar da suka hada da Abdullahi Wali, Mr Medan Kaigama da Mr David Majo

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) reshen Jihar Adamawa ta maye gurbin wasu shugabaninta uku da ta dakatar saboda zarginsu da yi wa jam'iyya zagon kasa da saba wasu dokoki.

A dai makon da ta gabata ne jam'iyyar ta dakatar da Alhaji Babangida Talase; Shugaban jam'iyyar na karamar hukumar Mayo-Balewa, Alhaji Saidu Naira; Sakataren Harkokin Kudi na Jam'iyyar da kuma Alhaji Aliyu Bakari; Mataimakin shugaban jam'iyyar na Adamawa Central saboda yunkurin janye karar da jam'iyyar ta shigar a kotu na kallubalantar nasarar Gwamna Ahmadu Fintiri na jam'iyyar PDP a zaben da ta gabata.

DUBA WANNAN: Sunaye da mukami: An zabi sabbin shugabanni a Kannywood

Sanarwar da Sakataren Yada Labarai na jam'iyyar, Honarabul Mohammed Abdullahi ya fitar ya ce an nada Abdullahi Wali, tsohon jami'i a jam'iyyar domin jagorantar mazabar Adamawa Central a matsayin shugaban jam'iyya.

A cewar sanarwar, Mr Medan Kaigama wadda shine mataimakin Sakataren Kudi na jam'iyyar zai kama aiki a matsayin mukadashin Sakataren Kudi na jam'iyyar a jihar yayin da Mr David Majo, mataimakin shugaban jam'iyyar na karamar hukumar Mayo-Belwa zai cigaba da aiki a matsayin mukdashin shugaban jam'iyyar na karamar hukumar.

Dukkan sabbin nade-naden za su fara aiki a ranar 16 ga watan Augustan 2019.

Ana sa ran za su cigaba da rike mukamansu na tsawon watanni shida da aka dakatar da tsaffin shugabanin biyu wato Saidu Naira da Babagida Talasai yayin da shi kuma Aliyu Bakari an dakatar da shi na ba tare da kayyade lokaci ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel