Sabon salo: Wadanda suka yi garkuwa da dan limami sun karbi giya a madadin kudin fansa

Sabon salo: Wadanda suka yi garkuwa da dan limami sun karbi giya a madadin kudin fansa

- An samu mabanbanta bayyanai kan ceto yaron limamin garin Ode-Omi da wasu abokansa biyu daga masu garkuwa suka sace

- Rundunar 'Yan sandan Najeriya reshen jihar Ogun ta ce ba a biya kudin fansa ba kafin ceto matasan uku

- Amma majiya daga iyalan wadanda aka yi garkuwa da su sun ce an biya N3.5m, katon din giya, doya, manja da man gyada

An samu karin haske kan yadda masu garkuwa da mutane suka sako wasu mutane uku da suka sace a karamar hukumar Waterside da ke jihar Enugu.

Majiya daga iyalan daya daga cikin wadanda aka sace ya shaidawa manema labarai a ranar Litinin cewa masu garkuwa da mutanen sun karbi kudi naira miliyan 3.5, katon din giya (Schnapps), lita 30 na manja da doya guda 10 kafin suka sako wadanda suka sace.

DUBA WANNAN: Sunaye da mukami: An zabi sabbin shugabanni a Kannywood

Rundunar 'Yan sanda a jihar a ranar Juma'a da ta gabata ta ce ta ceto dan gidan babbn limamin Ode-Omi, Abdulazeez Sanusi da wasu matasa biyu - Adams Bamidele da Jelili Adams da aka sace a ranar Lahadi.

An sace matasan uku ne a ranar jajiberin El-el Adha a garin Ode-Omi da ke kan iyakar jihar Legas da Ogun.

Amma Kwamishinan 'Yan sandan jihar, Bashir Makama ya ce ba a biya kudin fansa ba kafin ceto su.

Sai dai majiyar ta ce, "Masu garkuwa da mutanen sun karbi naira miliyan 3.5, katon din schnapps, lita 30 na manja, doya guda goma da lita biyar na man gyada."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel