Farawa da Bismillah: 'Yammata 15 sun amsa tayin Adam A Zango na fitowa a sabon fim din sa saura 15 a fara tantancewa
- Jim kadan bayan ya nemi 'yammata masu sha'awar shiga fim a shafinsa na Instagram cikin wani bidiyo
- Yanzu haka dai jarumi Adam A Zango ya samu 'yammata har guda goma sha biyar da suka nuna ra'ayin fitowa a sabon fim nasan
- Haka kuma ana jiran sauran guda goma sha biyar su cika wannan fam kafin ya fara tantance wacce zai dauka ta fito a fim din
Bayan fitowar jarumin a wani sabon bidiyo da ya sanya a shafinsa na Instagram yana kira ga 'yammata 'yan kasa da shekara 18 masu sha'awar shiga fim su cika wani fam domin daukarsu a wani sabon shiri da zai fara yi, yanzu dai akwai alamun hakar jarumin ta kusa cimma ruwa, inda aka samu 'yammata yara shataf guda goma sha biyar suka nuna ra'ayinsu akan wannan sabon fim nashi.
'Yammatan sun cika fam nashin sannan sun sanya hotunansu a cikin shafin domin jarumin ya zaba ya tantance wacce ta dace da wannan shirin nasa, sai dai kuma an bayyana cewa sai 'yammatan sun kai guda talatin za a fara tantancesu.
KU KARANTA: Sai da na biya yarinyar dake zargina da yi mata fyade miliyan 136 don tayi shiru da bakinta - Cristiano Ronaldo
A halin yanzu dai 'yammatan suna ta faman tururuwar cika wannan fam na jarumin.
Jiya ne dai jarumin ya fito a shafinsa na Instagram yake magana akan 'yammata da suke da bukatar shiga fim, ya bayyana cewa wannan dama ce a garesu, domin kuwa yana shirin fara daukar wani sabon fim wanda yake so ya sanya sabuwar fuska a ciki.
Wannan lamari dai na jarumin ya jawo kace nace matuka a shafukan sada zumunta, inda wasu ke ganin cewa jarumin na kokarin bata tarbiyar 'yammata Musulmai ne na arewacin Najeriya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng