Bayan ya cika shekaru 92, Dahiru Bauchi ya fadi yadda ya zama babban malamin Tijjaniya

Bayan ya cika shekaru 92, Dahiru Bauchi ya fadi yadda ya zama babban malamin Tijjaniya

Sheikh Dahiru Usman Bauchi, dattijo ne mai shekaru 92 a duniya kuma jigo a darikar Tijjaniya sannan mataimakin shugaban kwamitin koli na kungiyar malaman da ke bayar da fatwa a addinin Musulunci a Najeriya.

A wata hira da ya yi da dan wakilin jaridar The Punch, Armstrong Bakam, Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana wasu abubuwa dangane da rayuwarsa.

Da yake amsa tambaya a kan yadda ya zama babban malamin Tijjaniya, Sheikh Bauchi ya bayyana cewa, "ni bafulatani ne da aka haifa ranar 28 ga watan Yuni na shekarar 1927 a garin Nafada (da yanzu ke jihar Gombe), amma ni dan asalin garin Kwankiyel ne da ke karamar hukumar Darazo a jihar Bauchi.

"Na yi dukkan karatuna na addini a karkashin kulawar mahaifina, har na haddace Qur'ani, kuma ta hannunsa ne na karbi darikar Tijjaniya. Shi mahaifina ya karbi darikar Tijjaniya ne ta hannun wani mutum mai suna Alhaji Gwani Abba.

"Daga baya sai mahaifina ya bani izinin na tafi duk inda nake so domin zurfafa ilimina na addini da haddar Qur'ani.

DUBA WANNAN: Waiwaye: Yadda aka kori Zakzaky daga jami'ar ABU saboda haddasa rikici a shekarar 1979

"Bayan na bar gida ina yawon neman ilimi ne sai wataran na hadu da daya daga cikin shugabannin darikar Tijjaniya na duniya, sunansa Alhaji Ibrahim Kaulaha, dan kasar Senegal. Bayan mun hadu sai na bi shi, kuma a wurinsa na koyi abubuwa da yawa."

Sheikh Bauchi ya kara da cewa, "Kaulaha fitaccen mutum ne da kowa ya san shi."

Kazalika, ya bayyana cewa ya yi auren farko a shekarar 1948 kafin daga baya ya kara wasu aure tare da haifar 'ya'ya kusan 70 da jikoki da dama, wadanda ya ce dukkansu mahaddata Qur'ani ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel