Ambaliyan ruwa ya karya gadar da ta shiga tsakanin jahar Adamawa da Boko Haram

Ambaliyan ruwa ya karya gadar da ta shiga tsakanin jahar Adamawa da Boko Haram

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya sauka a jahar Adamawa ya yi sanadiyyar karyewar wata gadar kankare da ta hada karamar hukumar Madagali da karamar hukumar Michika da garin Yola na jahar Adamawa.

Haka zalika jaridar Sahara Reporters ta ruwaito wannan gadar ce ta shiga tsakanin jama’an Madagali-Michika da yan ta’addan kungiyar Boko Haram, bugu da kari a dalilin karyewar wannan gadar, babu wata hanya da ababen hawa zasu bi su shiga kananan hukumomin biyu daga Najeriya.

KU KARANTA: Matawalle ya sanar da sunan sabon shugaban ma’aikatan jahar Zamfara

Shi dai wannan gada da aka ginashi a garin Dilchim cikin karamar hukumar Michika shine kadai gadan daya rage a cikin gadojin da suka hada yankin da Michika da Madagali da garin Yola, babban birnin Yola. Ga shi kuma kananan hukumomin na makwabtaka da Dajin Sambisa, yanzu kuma babu gadar tsira.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a shekarar 2014 da Boko Haram ta kama kananan hukumomin jahar Adamawa guda 7 ne Sojoji suka karya gadar Kudzum dake kilomita 2 daga gadar Dilchim don dakatar da yan ta’adda daga shiga garin Yola.

Daga bisani a shekarar 2015 gwamnatin jahar Adamawa ta bayar da kwangilar sake gina gadar Kudzum, amma har yanzu ba’a kammala aikin ba, wanda hakan ya yi matukar harzuka gwamnan jahar Ahmadu Fintiri, amma Injiniyan dake kwangilar, Joshuwa Yakubu ya bayyana cewa rashin tsaro ne yasa basu kammala aiki ba.

Sai a yanzu da ake kukan rashin kammala aikin sake gina gadar Kudzum, ruwa ya lalata gadar Dilchim, wanda tabbas zai jefa jama’an yankin Madagali-Michika cikin halin rashin tsaro sakamakon hanyar da za’a bi a kai musu dauki, ga shi kuma suna kusa da dajin Sambisa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel