Ambaliyan ruwa ya tafka ma manoma mummunar barna a jahar Jigawa

Ambaliyan ruwa ya tafka ma manoma mummunar barna a jahar Jigawa

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da ake samu a daminar bana, musamman a watan Agusta ya lalata dubun dubatan gonakan manoma a jahar Jigawa, musamman a karamar hukumar Malammadori.

Rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN ta bayyana cewa wannan lamari ya faru ne a wasu kauyuka guda 9 dake karamar hukumar Malammadori, inda ruwan ya lalata akalla eka 12, 000 na gonakan jama’a.

KU KARANTA: Matawalle ya sanar da sunan sabon shugaban ma’aikatan jahar Zamfara

Daga cikin gonakan da ambaliyan ruwan ya shafa akwai na shinkafa, rogo, ridi da kuma dawa, kamar yadda kansilan mazabar Tashena, Yunusa Bulama ya shaida ma majiyar Legit.ng.

Kansila Bulama ya tabbatar da haka ne yayin da dan majalisa mai wakiltar Kaugama/ Malammadori a majalisar wakilan Najeriya, Maki Yalleman ya kai musu ziyarar jaje, inda yace lamari ya auku ne a ranar Juma’a, 16 ga watan Agusta.

Bulama ya bayyana kauyukan da lamarin ya shafa kamar haka; Tashena, Kadumunbari, Hadyan, Azumu, Kadumantudu, Dowawa, Dososo, Allahyayi, da unguwar Jama’are. Ya cigaba da cewa eka 8,000 na shinkafa sun lalace, yayin da eka 4,000 na rogo, dawa da ridi suka lalace.

Da yake jajanta musu, shugaban karamar hukumar, Hussaini Birnin Kudu yace sun samar da buhuhuna 5,000 don cikasu da kasa domin su zamo kariya ga gonakai a bakin kogin Hadejia sakamakon ruwan kogin na karuwa.

Daga karshe dan majalisa Yalleman ya yi alkawarin tallafa ma wadanda lamarin ya shafa, sa’annan ya yi kira ga mutanen dake zaune a bakin ruwa dasu gaggauta tashi don tsira da rayuwarsu da dukiyoyinsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel