Falmata Bulama: Iyaye da 'yan uwan matar aure sun juya mata baya saboda kubutar da mijinta daga kungiyar Boko Haram
Falmata Bulama Umar, wacce aka fi sani da 'Yakarama', wata matar aure ce mai shekaru 30 a duniya da ke da 'ya'ya 10 da kuma kula da wasu yaran su 20 a matsayin na riko kafin a gano iyayensu a mika su gare su.
Falmata, 'yar asalin garin Modube da ke kasar Kamaru, na zaune tare da mijinta, Bulama Umar, a garin Wajere mai makwabtaka da Banki a karamar hukumar Bama, jihar Borno.
Tsawon shekaru bakwai kenan yanzu da iyaye da 'yan uwan Falmata suka katse zumunci da duk wata hulda da ita saboda ta kubutar da mijinta daga hannun 'yan kungiyar Boko Haram da suka kama shi. Sai dai, danginta na zargin cewa mijin nata dan kungiyar Boko Haram ne.
Daya daga cikin 'yan uwan Falmata, wanda mamba ne a kungiyar 'Yansakai' a Banki, ya taba yi mata barazanar cewa zai kashe ta.
"Lamarin ya faru ne a shekarar 2012 lokacin da mayakan Boko Haram suka ci garin Wajere da yaki. suka yi kuma niyyar kama ni a kan dalilin da har yanzu ban sani ba.
"Mu na da isashen lokacin gudu wa a lokacin da mayakan kungiyar Boko Haram suka kawo harin, amma duk kokarina na son ganin na shawo kan mijina a kan mu gudu, mu bar a gari, a banza saboda mijina ya ce a matsayinsa na Dagacin gari, wakilin jama'a, ba zai iya gudu ya bar jama'arsa ba.
"Daga karshe sai ni kadai na gudu, na koma garin mu, Modube, wurin iyayena kafin daga bisani na kara gaba zuwa Yawunde, babban birnin kasar Kamaru," a cewar Falmata.
Falmata ta bayyana cewa daga bisani ta samu labarin cewa 'yan Boko Haram sun kama mijinta saboda ya umarci ta gudu a lokacin da suka kawo hari, ta kara da cewa daga nan ne ta ci alwashin koma wa domin ta kubutar da shi daga hannun mayakan kungiyar Boko Haram.
A cewar Falmata, bayan ta koma gida tare da sanar da iyayenta kudirin da ta ke da shi, sai suka ce sam ba zata yiwu ba, sai dai ta zabi daya tsakanin iyaye da miji, bayan sun yi zargin cewa dan kungiyar Boko Haram ne.
Ta kara da cewa a cikin wannan yanayi ne, yayanta ya yi barazanar cewa zai kashe ta saboda tana son taimakon mijinta da suke zargi da zama mamba a kungiyar Boko Haram.
Falmata ta bayyana cewa, kwana da daya kacal ta kara bayan faruwar hakan, ta bar gida tare da koma wa Wajere domin neman mijinta.
A cewar ta, sai da ta shafe tsawon sati biyu tana nema kafin ta gano jejin da mayakan Boko Haram suka boye mijinta. Duk da ta ki bayyana dabarun da ta yi amfani da su, Falmata ta ce ta samu nasarar kubutar da mijinta kuma yanzu suna zaune tare abinsu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng