Hawaye sun kwarara yayin da rundunar Soja ta binne jami’anta 5 da Boko Haram ta halaka

Hawaye sun kwarara yayin da rundunar Soja ta binne jami’anta 5 da Boko Haram ta halaka

Rundunar Sojan kasa ta gudanar da jana’izar dakarunta guda 5 a ranar Juma’a, wadanda suka mutu a yayin arangama da mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Sojojin sun hada da Kanal Kenneth Elemele, Las kofur Ajijola Sunday, Oguntuase Ayo, Dimos Danial da kuma Akinola Ayoola, wadanda aka binnesu kamar yadda dokokin addinin kirista ya tanadar a makabartar Sojoji dake barikin Maimalari.

KU KARANTA: Zaben 2019: Atiku ya bukaci kotu ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zabe

Sabon kwamandan yaki na Operation Lafiya Dole, Olusegun Adeniyi ne ya jagoranci jana’izar Sojojin, inda ya jaddada manufar rundunar na kawo karshe ayyukan Boko Haram a yankin Arewa maso gabas.

“A madadin babban hafsan Sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ina taya yan uwa da abokan arzikin Sojojin nan 5 alhinin mutuwarsu, ba mu ji dadin abinda ya faru ba, amma ina tabbatar muku basu mutu a banza ba, sun sadaukar da rayukansu ga Najeriya ne.

“Sun zamto abin alfahari kuma yan kasa nagari, basu gudu daga abokan gaba ba, sai dai ma suka tunkareshi kai tsaye ba tare da tsoro ba, ina tabbatar muku ba zamu yi kasa a gwiwa ba, kuma ba zamu sassauta ma Boko Haram ba, zamu dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso gabas.” Inji shi.

Haka zalika Adeniyi ya bayyana cewa akwai tsari mai kyau da zai kula da walwalar iyalan mamatan domin samun hakkokinsu a lokacin daya kamata, don haka ya yi kira ga iyalan mamatan dasu nemi karin bayani daga wajensa ko kwamandan shiyya ta 2 game da hakkokin yan uwan nasu.

Daga karshe rundunar ta mika tutocin Najeriya ga dukkanin iyalan mamatan, wanda hakan alamace ta girmamawa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel