El-Zakzaky na fama da matsanancin guba, zai iya mutuwa a koda yaushe - Inji Diyarsa

El-Zakzaky na fama da matsanancin guba, zai iya mutuwa a koda yaushe - Inji Diyarsa

Suhaila, diyar Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, Shugaban kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN), wacce aka fi sani da Shi’a, tace mahaifinta na fama da matsanancin guba a jikinsa wanda ka iya sanadiyar mutuwarsa.

A wata hira da shafin BBC, ‘yar El-Zakzaky tace babban malamin ya cancanci samun kulawar likitoci a tsanaki.

“Na damu matuka, musamman saboda gubar da ke jikinsa,” inji ta.

“Likitocinsa sunce idan ya kai wani mataki a jikinsa yana iya fara gazawa sannan cewa abun tsoro ne matuka saboda hakan na nufiun yana iya mutuwa a koda yaushe."

Suhaila tace mahaifinta ya fada mata cewa bai ji dadin yadda aka tsaurara matakan tsaro a asibitin Medanta, New Delhi, inda ya je yin magani ba.

Shugaban na IMN ya bar Najeriya zuwa kasar Indiya a ranar Litinin biyo bayan damar zuwa yin magani da wata babbar kotun Kaduna ta bashi.

Sai dai kuma a ranar Laraba, El-Zakzaky ya koka cewa halin da ya tsinci kansa a ciki a Indiya ya fi na Najeriya tabarbarewa.

KU KARANTA KUMA: El Zakzaky na shirin neman magani a wata kasa bayan Indiya

Yace an hana shi ganin likitocin da yake son gani yayinda jami’an tsaro suka turke shi.

Sai dai gwamnatin tarayya ta karyata ikirarin malamin, inda ya zarge shi da son bijirewa, da kuma gabatar wasu bukatu marasa amfani, ciki harda son zama a babban otel na lasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel