Tirkashi: Sabon rikici ya barke tsakanin Muneerat Abdulsalam da mawaki Misbahu M Ahmad

Tirkashi: Sabon rikici ya barke tsakanin Muneerat Abdulsalam da mawaki Misbahu M Ahmad

- Wani rikici ya barke tsakanin jarumi Misbahu M Ahmad da Muneerat Abdulsalam a shafin Instagram

- Rikicin ya biyo bayan wata magana da Misbahu Ahmad yayi akan Muneerat Abdulsalam inda ya bayyana cewa irinsu 'yan wuta ne

- Wannan dalili ne yasa Muneerat Abdulsalam ta wallafa wani rubutu a shafinta na Instagram inda ta dinga surfawa jarumin zagi

Muneerat Abdulsalam ita ce macen da tayi suna akan maganganu na batsa a shafin sanya bidiyo na YouTube, inda ta bayyana cewa abinda take yi gyaran aure ne, kuma ta wallafa a shafinta na Instagram a safiyar ranar Asabar, akan mawaki Musbahu M Ahmad.

Jarumar ta wallafa maganganun cin mutuncin da zagi a matsayin martani ga wata magana da Musbahun yayi wacce alamu ke nuni da cewa ya tura ne a shafin WhatsApp, amma kuma sakon ya fita har yaje ga kunnen ita Muneerat, inda a cikin abinda Musbahun yake cewa ya bayyana Muneerat da ire-irenta a matsayin 'yan wuta.

KU KARANTA: Tirkashi: Bidiyon yadda Aisha Idris ta dinga tona asirin Ali Nuhu, inda ta bayyana abubuwan da yake aikatawa a boye

Ga sakon da Muneerat din ta ce a shafinta na Instagram:

"Shege ya sha wahala har fuskarsa ta zama kala daban daban, ya zo wai shima bari ya nemi suna, to ai ba dani ta bare maka ba, da yake kai dakike ne ba kasan cewa Blogging daban yake da yin fim ba.

"Zanyi misali da kai Misbahu Ahmad yau da kai na tashi, sai ka gayamin ko kunyi shawara da mahaliccina ya tabbatar maka da cewa ni 'yar wuta ce.

"Shege tun ina 'yar shekara biyar kake yin fim din Hausa amma har yau baka yi suna ba, sa'o'inka duk sun zama abin alfahari a duniya kai kana nan da fuska kamar amai."

Haka kuma Muneerat ta sake wallafa wani sako a shafin nata, inda ta ce:

"Kana nan kana bina a Facebook kana so nayi maka magana tun shekarar 2016 bana kula ka, sannan aka wayi gari har wai kana zagin mutane. Ni na taba gaya maka ina wasan Hausa ne, shawarwari da auren dana gyara har zuri'arka su kare ba wanda ya isa yayi, Allah wadaran irinku.

"Yanzu kaje ka nemi taransfoma ka runguma, saboda yanzu ka fara ganin takaici da bacin rai, saboda kowa ya ganka ya san neman suna kake yi, don yanzu an daina yi da kai a Kannywood."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel