Miji, mata da 'ya'yansu biyu sun mutu bayan cin abincin Sallah a Kebbi

Miji, mata da 'ya'yansu biyu sun mutu bayan cin abincin Sallah a Kebbi

Wani miji da matarsa tare da 'ya'yansu sun mutu bayan sun kammala cin wani abinci da aka sarrafa daga garin dawa yayin bikin Sallah a karamar hukumar Danko-Wasagu a jihar Kebbi.

Rahotanni sun bayyana cewa mata da mijin tare da 'ya'yansu sun yi korafi da ciwon ciki kafin daga bisani su mutu bayan sun gama cin abincin.

Wani mazaunin yankin da abin ya faru mai suna Jeremiah Audu ya sanar da jaridar Daily Trust cewa Maigidan ya sayo garin dawar ne daga wata kasuwa a yankin Mahuta, kuma sun yi amfani da ita domin yin tuwon sallah.

A cewar Audu, "bamu san me suka ci ba. Kawai mun ji ihu daga cikin gidan, ko a lokacin da muka garzaya gidan tuni mijin da matar tare da 'ya'yansu na murkususu cikin ciwo. Kafin mu iya basu wani agajin gagga wa, matar da yaran biyu duk sun mutu."

Ya kara da cewa mijin bai mutu nan take ba, sai bayan an garzaya da shi zuwa babban asibitin garin Mahuta.

DUBA WANNAN: Tsohuwa fitacciyar jarumar fim din Indiya ta kashe diyarta budurwa, ta kashe kan ta (Hotuna)

"Kafin ya mutu ne yake bayyana cewa sun ci tuwon sallah ne aka tuka daga garin dawar da ya sayo a kasuwa, sakamakon hakan ne duk cikinsu ya fara ciwo," a cewar Audu.

Ya bayyana cewa mutuwar mutanen hudu ta saka gaba daya al'ummar yankin cikin rudani da tashin hankali a ranar Sallah.

"Dukkan jama'ar garin mu sun shiga cikin damuwa saboda mutuwarsu. Mutuwa ce mai ciwo, saboda duk sun mutu ne a lokaci guda," a cewarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel