Yadda wani matashi mai halin bera ya debo ruwan dafa kansa daga satar waya

Yadda wani matashi mai halin bera ya debo ruwan dafa kansa daga satar waya

Wata karamar kotu dake zamanta a garin Kabusa, na babban birnin tarayya Abuja, ta yanke ma wani matashi dan shekara 20 hukuncin daurin shekaru 7 cur tare da horo mai tsanani bayan ta kamashi da satar wayar salula.

Rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya, NA, ta bayyana cewa matashin mai suna Sadiq Mohammed ya saci wata wayar salula kirar Tecno da wata na’urar sauraron wakoki mai suna MP3 Music player ne, dukkaninsu mallakin wani mutumi Isa Gani.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Buhari zai kwace NEPA daga hannun yan kasuwa, zai mayar musu da kudinsu

Dansanda mai shigar da kara, Mahmud Lawal ya bayyana ma kotu cewa Isa Gani dake zaune a unguwar Hausa, Garki Abuja ya kai kara ofishin Ynsanda dake Garki Abuja a ranar 6 ga watan Agusta, a kan cewa Sadiq ya sace masa wayarsa da MP3.

Dansanda Lawal ya cigaba da shaida ma kotun cewa darajar wayar Tecno da MP3 sun kai N16,000, sa’annan yace wanda ake tuhuma da satar, Sadiq ya amsa laifinsa yayin da Yansanda suke gudanar da bincike a kansa.

Don haka Dansanda mai kara, Lawal, ya nemi kotu ta hukunta Sadiq daidai da laifin daya aikata kamar yadda sashi na 288 na kundin hukunta manya laifuka ta tanadar. Shima a nasa jawabin, Sadiq, ya amsa laifinsa na tafka sata.

Bayan sauraron dukkanin bangarorin, sai Alkalin kotun, mai sharia Ibrahim Kagarko ya yanke ma Sadiq hukuncin zaman kurkuku na tsawon shekaru 7 ba tare da zabin biyan ko sisi a matsayin tara ba, ma’ana sai ya kwashe shekaru 7 babu kakkautawa a gidan yari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel