Da dumi-dumi: El-Zakzaky ya sake magana daga kasar Indiya (bidiyo)

Da dumi-dumi: El-Zakzaky ya sake magana daga kasar Indiya (bidiyo)

Shugaban kungiyar yan uwa Musulmai na Shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya sake sabon jawabi daga kasar Indiya inda ya je yin magani.

A cikin sabon bidiyon El-Zakzaky ya zargi gwamnatin Najeriya da shirga karairayi dangane da asibitin da aka kai su.

Yace: “Bayanin da nayi da farko shekaran jiya ban sa kwanan wata ba, wato ranar Talata bayan mun baro Abuja Litinin, mun iso Indiya Talata, kuma a ranar ne nayi Magana ta farko.

“A yau Alhamis ya zama dole na sake wasu bayani, naji ance mahukuntan Najeriya sun ba da wasu bayanai wanda suka shiga kara-karai, ko dai a gasgata ni ko kuma a gasgata gwamatin Najeriya akan wannan al’amari.

“Mu abunda muka fahimta das u tun farko shine su so suka yi su kai mu asibitin ne shine suke cewa mu da kanmu ne muka zabi asibitin, kafin ma mu zo sun shirya jirgin sun a gashin kansu cewa za su kai mu wani asibiti mai suna fotis, sai muka ce ai ga wanda mu muka zaba.

KU KARANTA KUMA: Kannywood: Adam Zango ya yi martani akan kamun jarumi Sanusi Oscar

"Sai suka ce ai su sun bincika sun ga cewa wannan fotis din ya fi, toh dam un yarda das hi din suka kaimu, amma anan abunda suke gaya mana mu shine cewa gwamnatin kasar ku ce ta zabi wannan, inda kuma achan suna fada ma jama’a cewa mune muka zabi asibitin.

“Sannan kuma cewa gwamnatin Najeriya ta roki ta kasar Indiya akan ta basu kariya saboda za su kawo wasu mutane ne da ake tuhuma da miyagun laifuffuka da kuma dogaro da rashin lafiyar dab a a sani ba."

Kalli bidiyon a kasa domin jin cikakken jawabin Sheikh El-Zakzaky:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel