Kisan 'Yan sanda a Taraba: An kama dan sanda a Bauchi saboda ya yi barazanar daukan fansa kan sojoji

Kisan 'Yan sanda a Taraba: An kama dan sanda a Bauchi saboda ya yi barazanar daukan fansa kan sojoji

An kama wani jami'in dan sandan Najeriya bayan ya yi ta wallafa rubutu a Facebook inda ya yi barazanar daukan fansa kan sojojin Najeriya saboda kashe abokan aikinsa 3 da su kayi a Taraba.

Kwamishinan 'yan sanda ya shaidawa BBC cewa za a dauki matakan hukunci kan Sunday Japhet da yanzu ya ke tsare a jihar Bauchi.

A makon da ta gabata, sojojin sun kashe 'yan sanda uku tare da farar hula guda daya bayan da suke bude musu wuta a motar da suke dauke da wani mai garkuwa da mutane. Sojojin sun ce sunyi tsamanin masu garkuwa da mutane ne a cikin motar.

DUBA WANNAN: An fitar da sunaye da hotunan 'Yan sanda 3 da sojoji suka bindige a Taraba

Japhet ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa: "Ba zai yiwu a bari a kashe su ba kawai a bar iyalansu da shan wahala babu dalili."

A wani rubutun da ya wallafa kuma, ya zazagawa Shugabankasa, mataimakin shugaban kasa da shugaban 'yan sanda zagi.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Yobe wanda Japhet ke karkashinsa ya ce rundunar tana son sanin 'manufansa na wallafa wadannan rubutun ne".

Wata sanarwa da ta karade shafukan sada zumunta da ba a tabbatar da sahihancin ta a makon da ta gabata ta shawarci 'sojoji su dinga takatsantsan yayin cudanyarsu da 'yan sanda' bayan kisar da sojoji su ka yi wa 'yan sanda a Taraba.

Tuni dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa kwamiti na musamman don binciken ainihin abinda ya faru har aka kashe 'yan sandan 3 da farar hula guda daya kuma wanda ake zargin da satar mutane ya yi batar dabo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel