Tirkashi: Bidiyon yadda Aisha Idris ta dinga tona asirin Ali Nuhu, inda ta bayyana abubuwan da yake aikatawa a boye

Tirkashi: Bidiyon yadda Aisha Idris ta dinga tona asirin Ali Nuhu, inda ta bayyana abubuwan da yake aikatawa a boye

- Aisha Idris ta bayyana wasu halayen jarumi Ali Nuhu da yake aikatawa a boye

- Ta ce da tana mutukar kaunar fina-finan shi amma yanzu babu wanda ta tsani kalla kamar shi

- Ta ce ta san yana da hannu a kama jarumin fina-finan Hausa da aka yi Sunusi Oscar

A cikin wani bidiyo da yake ta faman yawo a shafukan sada zumunta, ya nuna yadda Aisha Idris wacce ke zaune a kasar Jamus take magana akan fitaccen jarumi Ali Nuhu da irin shawarwarin da ta bashi.

Ga dai abinda budurwar take cewa:

"Ali Nuhu lokacin da kake fada da Adam A Zango na baka shawara na ce na san ka girme ni amma ina so ku daina wannan hayaniyar, sai kake ce mini ai kai baka taba wallafa wani abu ba game da wannan rikici ba na ce eh hakane, ka ce kai dama baka fada kowa nace dama shawarace na kawo.

KU KARANTA: Ta faru ta kare: Daga yau na daina fim har sai gwamnatin Ganduje ta sauka - Naburaska

"Ali Nuhu kai munafikine, saboda kai baka fitowa kayi magana kamar sauran 'yan fim, kai babban munafikine kana yin abubuwanka a boye, duk 'yan fim tsoronka suke ji, kai ba Allah ba, ko Fir'auna yayi zamaninsa ya gama.

"Ku daina tsoron Ali Nuhu daga yanzu 'yan fim saboda shi ba kowa bane. Ni Aisha Idris na fito na fada, idan kuma nima zaka sa a kamani zan baka adireshin gidana a Germany kasa azo a kama ni, amma wallahi kai munafiki ne.

"Da fina-finanka suna burgeni, amma yanzu wallahi na tsane ka. Ko fina-finai yanzu iya naka kawai ake nunawa a gidan kallo, saboda kawai Ganduje ya ci mulki.

"Sunusi Oscar da kuka saka aka kama dan adam ne kamarka, idan ka san yau baka san gobe ba, wata rana kowa mutuwa zai yi, saboda haka kaji tsoron Allah.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel