Ta faru ta kare: Daga yau na daina fim har sai gwamnatin Ganduje ta sauka - Naburaska

Ta faru ta kare: Daga yau na daina fim har sai gwamnatin Ganduje ta sauka - Naburaska

- Fitaccen jarumin fina-finan Hausa Mustapha Naburaska ya bayyana cewa daga rana irin ta yau ya daina wasan fim din Hausa

- Jarumin ya bayyana hakan ne inda ya ce ba zai cigaba ba har sai gwamnatin jihar Kano ta yanzu ta sauka daga mulki

- Ya ce ya dauki wannan mataki ne sakamakon abinda aka yiwa abokin sana'arshi jarumi Sunusi Oscar, inda har lamarin ya kai ga kaishi gidan yari

Jarumin fina-finan Hausa Mustapha Naburaska ya shaidawa masoyansa cewa daga rana irin ta yau ya daina yin shirin fim, sannan kuma ya fita daga kungiyar Kannywood har sai lokacin da Allah ya kawo karshen gwamnatin jihar Kano ta gwamna Ganduje.

A cikin wani bidiyo da jarumin ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, ya bayyana cewa ya dauki matakin ne sakamakon abinda aka yiwa abokin sana'arshi Sunusi Oscar.

KU KARANTA: Tashin hankali: Wata mata ta yiwa saurayin 'yarta wanka da tafasashen ruwa bayan ta yaudareshi ya je gidanta

Idan ba a manta ba gwamnatin jihar Kano ta sa an kama Sunusi Oscar ne bayan da wasu suka kai maganar da yayi wajen hukuma inda aka kama shi aka mikawa kotu.

Jarumin ya bayyana cewa akwai sa hannun wasu jaruman Kannywood a cikin wannan lamarin da ya faru da Sunusi Oscar amma kuma bai bayyana ko suwaye ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng