El-Zakzaky ya saba dokokin belinsa a India - FG

El-Zakzaky ya saba dokokin belinsa a India - FG

A daren jiya ne gwamnatin tarayya tayi ikirarin cewa shugban kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN), Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya saba dokokin belin da kotu ta bashi kafin ya tafi kasar India neman magani.

Jawabin da Farmanen Sakataren Ma'aikatar Watsa Labarai, Deaconess Grace Isu Gekpe, ta fitar ya ce El-Zakzaky ya nemi a mika masa fasfo dinsa tafiya kasashen waje kuma ya bukaci a bar shi ya zauna otel mai daraja ta 1 a maimakon asibitin.

Jawabin ya kuma ce shugaban na IMN ya bukaci a bari ya tafi duk inda ya ke so sannan a bari ya dinga ganawa da kowanne irin bako da ya zo ganinsa.

DUBA WANNAN: Yadda Iran tayi amfani da kudi wajen jan ra'ayin dan uwa na - Yayan Zakzaky

Sanarwar ta ce irin wadannan abubuwan ne suka fusata gwamnatin kasar India har su kayi barazanar mayar da shi Najeriya.

Sanarwar ta ce a yayin da suka isa Dubai a hanyarsu ta zuwa India ne El-Zakzaky ya fara bayyana makircin da ke zuciyarsa na kin biyaya da sharuddan da kotu ta gindaya masa.

Wani sashi na sanarwar ya ce "Ya nemi a mika masa fasfo dinsa amma jami'an kasar ba su amince da hakan ba. Lamarin ya yi muni har da farko su ka ki fara duba shi.

Sanawar ta kuma ce, "bugu da kari, ya nemi a bar shi ya tafi duk inda ya ke so har ma da neman a sauke shi a otel mai daraja ta 1 kuma a bari ya dinga ganawa da bakin da ba a amince da su ba.

"An ki amincewa da hakan ne saboda tun farko neman magani ya zo ba wai yawon bude idanu ba. Ya kuma nemi a kasar India ta janye 'yan sandan da aka turo domin kulawa da shi."

Duk wadannan sabbin bukatun sun haifar da jinkiri wurin fara duba lafiyarsa inda India ta ce ba za bari ya yi amfani da kasar ta wurin tallata kungiyarsa ba.

Daga bisani gwamnatin Najeriya ta bawa kasar India hakuri ta kuma janyo hankulan kasashen duniya kan abubuwan da ke faruwa.

Daga karshe dai anyi sulhu kuma an bari likitocin da ya amince su fara duba shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel