Matar da ta bugawa 'yar ta guduma a goshi ta fuskanci fushin kotu

Matar da ta bugawa 'yar ta guduma a goshi ta fuskanci fushin kotu

Wata kotun Majistare da ke zamanta a Ikeja, a jiya Laraba ta bayar da umurnin cigaba da tsare wata mata mai shekaru 32 da aka yi ikirarin ta bugawa 'yar ta mai shekaru 11 guduma a goshin ta.

Matar mai suna Chinonso Michael mai zaune a unguwar Iwaya a Yaba Legas ta amsa cewa ta doki 'yar ta da sandan tuka tuwo na katako.

Sai dai Alkalin kotun, Olufunke Sule-Amzat ba ta gamsu da amsa laifan wacce ake tuhumar ba hakan yasa ba bayar da umurnin a cigaba da tsare ta a gidan yarin kirikiri.

DUBA WANNAN: Tsohon kwamishinan 'Yan sanda ya fadi wadanda ke daukan nauyin 'yan bindiga a Najeriya

Ta umurci 'Yan sanda su mika takardar da ya bunshi abinda matar da aikata zuwa ofishin direktan tuhumar masu laifi don ya bayar da shawara.

An dage cigaba da sauraron karar har zuwa ranar 30 ga watan Satumba.

Ana tuhumar wadda akayi kara da laifin duka da duka da ya haifar da rauni.

Dan sanda mai shigar da kara, ASP Benson Emeurhi ya ce wacce ake tuhumar da aikata laifukan ne a ranar 28 ga watan Yuli a gidansu da ke Iwaya.

Ya yi ikirarin cewa wacce ake tuhumar da doki diyarta da sandan tuka tuwa kuma ta buga mata guduma a goshi saboda ta fusata.

Mai shigar da karar ya yi ikirarin cewa makwabta ne suka cece diyarta.

Emeurhi ya ce daga nan ne aka kai kara ofishin 'yan sanda aka sanar da su abinda ya faru.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel