Zaman lafiya: Coci sun gayyaci Obasanjo wajen taron addu’a a Ibadan

Zaman lafiya: Coci sun gayyaci Obasanjo wajen taron addu’a a Ibadan

An gayyaci tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo da wasu Jama’a da dana wajen taron yi wa kasa addu’a da a ka shirya a Garin Ibadan a jihar Oyo. An yi wannan taro ne Ranar Laraba.

Sai dai Cif Olusegun Obasanjo bai samu halartar wannan taro ba, amma ya aika babban Wakili wanda ya tsaya masa a wannan zaman addu’o’i da a ka yi a Ranar 15 ga Watan Agusta, 2019.

Kamar yadda mu ka samu labari, Sha’irai fiye da 2000 wanda su ka kware a wake-waken coci su ka halarci wannan zama da a ka yi a wani babban coci mai suna Molete Baptist da ke Ibadan.

Dr. Doyin Okupe wanda ya taba aiki a matsayin Hadimin Olusegun Obasanjo a lokacin ya na mulki, shi ne wanda ya wakilce sa a wurin wannan taro inda a ka yi wa Najeriya addu’o’i.

A jawabin tsohon shugaba Olusegun Obasanjo, ya yabawa kungiyar GOMAN da ta shirya wannan zaman a addu’o’in kasa a Najeriya. Doyin Okupe shi ne wanda ya karanta wannan jawabi a taron.

KU KARANTA: Abin da ya sa tsohon Shugaba Obasanjo ya rubutawa Buhari wasika - Musa

Okupe a madadin Obasanjo ya ke cewa: “Ina mai matukar yabawa aikin GOMAN da kokarin tada Najeriya ta hanyar addu’o’i da ibada da ya yabo da kuma bauta, musamman a wannan lokaci.”

“Babu shakka mu na bukatar agajin Ubangiji domin ganin Najeriya ta cigaba da tafiya a tafarkin zaman lafiya, lumana, kwanciyar hankali da kuma cigaba da dai sauransu.” Inji tsohon shugaban.

Bayan tsohon shugaban kasar ya yi jawabi ta bakin Dr. Okupe, Misis Irene Osinbolu wanda ta wakilci gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ta mike ta karanto jawabin gwamnan a wurin.

Shugabar wannan kungiya ta GOMAN, Funmi Aragbaiye, ta bayyana cewa ta shirya wannan taron addu’a ne domin nemawa Najeriya mafita wajen Ubangiji a game da halin tsaro da a ke ciki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel