Ga irinta nan: Wani mutumi ya mutu a daidai lokacin da yake zina da wata bazawara a cikin gonar masara

Ga irinta nan: Wani mutumi ya mutu a daidai lokacin da yake zina da wata bazawara a cikin gonar masara

- Wani mutumi ya mutu a cikin gonar masara a lokacin da yake tsakiyar zina da wata bazawara mai shekara hamsin a duniya

- Bazawarar ta bayyana cewa mutumin mai shekaru talatin da biyar ya sha maganin karfin mazane wanda ya wuce gona da iri

- Matar dai ta sha zagi a wajen mutanen garin, inda suka zargeta da kokarin bata tarbiyar yaransu

Wani mutumi dan shekara 35 yayi wata irin mutuwa a lokacin da yake tsakiyar yin zina da wata bazawara mai shekaru 50 a cikin wata gonar masara dake Sachangwa-Chebyakwai, kusa da filin jirgin sama na Eldoret a kasar Kenya ranar Litinin dinnan da ta gabata.

An bayyana sunan mutumin da ya rasu din da Julius Kiptoo, inda aka ce yana ta shan giya har cikin dare a wani wajen shan giya a ranar Lahadi, daga baya kuma ya daidaita wata mata wacce ba zamu iya bayyana sunanta ba.

A lokacin da manema labarai suka je wajen da lamarin ya faru ranar Litinin dinnan da safe, an hango mutane suna ta kokarin shiga cikin gonar masarar domin ganin mutumin da ya rasu din.

Matar ta bayyanawa 'yan sanda yadda mutumin ya haukace wajen yin lalata da ita bayan ya sha maganin karin karfin maza.

KU KARANTA: Kudi masu gidan rana: Ina siyan tabar wiwi ta miliyan 15 a kowanne wata - Mike Tyson

"Mun nufi gida fa lokacin, amma sai ya kasa hakura inda ya nemi muyi a cikin gonar masarar na. Amma sai abin nashi ya wuce gona da iri, inda ya mutu kuma a take a wajen," in ji matar.

Ta ce daga baya ta kira makwabtansu, inda suka tabbatar da cewar mutumin ya mutu.

Jami'an 'yan sandan da suka je wajen da lamarin ya faru sun dauki gawarshi zuwa asibitin koyarwa na Moi domin gabatar da bincike.

Matar dai kuma ta zama abar zagi a kauyen inda suka dinga yi mata habaici suna cewa ta zama abar kwatance wajen bata tarbiyar yaransu, tunda har take lalata da saurayin da bai kaita a haife ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel