Kudi masu gidan rana: Ina siyan tabar wiwi ta miliyan 15 a kowanne wata - Mike Tyson

Kudi masu gidan rana: Ina siyan tabar wiwi ta miliyan 15 a kowanne wata - Mike Tyson

- Fitaccen dan wasan damben nan na duniya, Mike Tyson ya bayyana yawan tabar wiwin da yake sha a kowanne wata

- Ya bayyana cewa a wata yana kashe sama da dalar Amurka dubu arba'in, kimanin naira miliyan sha biyar kenan a kudin Najeriya

- An bayyana cewa tsohon dan wasan damben yana da gonar da yake shuka tabar wiwi a birnin California mai girman kadada arba'in

Fitaccen dan wasan damben nan na kasar Amurka, Mike Tyson ya bayyana cewa yana kashe dalar Amurka dubu arba'in ($40,000) kimanin naira miliyan sha biyar (N15,000,000), a kowanne wata akan tabar wiwi.

Yayi magana a wata kafa mai suna Hotboxin, kamar yadda jaridar The Mirror ta ruwaito, Iron Mike ya bayyana yawan tabar wiwin da yake sha a kowanne wata.

Haka kuma tsohon dan wasan NFL Eben Britton, wanda yake daya daga cikin makusanta ga Tyson, ya bayyana cewa: "Muna shan ton goma na tabar wiwi a kowanne wata."

KU KARANTA: Ka aure ni ko na kashe kaina - Bidiyon Budurwar da ta dinga suma tana rokar saurayinta ya aureta

Tsohon wanda ya lashe gasar damben ta duniya ya mallaki gonar tabar wiwi mai girman kadada arba'in a kusa da birnin California, wanda ya bude bayan kasar Amurka ta hallata shan tabar wiwi.

Haka kuma fitaccen dan wasan mai shekaru 53 ya bude wata makaranta wacce yake koyar da yadda ake shuka tabar wiwin, wacce ya sanyawa suna 'The Tyson Cultivation School' a turance.

Kamar yadda hasashe ya nuna, Muke Tyson yana samun dalar Amurka miliyan uku kowacce shekara. Sannan ya samu sama da dala miliyan dari uku a lokacin da yanke wasan dambe, daga baya kuma ya dawo bashi da ko sisi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel