Wata budurwa ta shararawa saurayinta mari a bainar jama'a saboda ya ki amsa cewa zai aure ta bayan soyayyar shekaru 6

Wata budurwa ta shararawa saurayinta mari a bainar jama'a saboda ya ki amsa cewa zai aure ta bayan soyayyar shekaru 6

- Wata budurwa ta tara jama'a domin ta mika bukatar neman aure ga saurayin ta da suka shafe lokaci mai tsawo suna soyayya

- Sai dai, saurayin nata, da suka shafe tsawon shekaru 6 tare, ya ki amsa mata cewa zai aure ta kamar yadda ta bukata.

- Budurwar ba ta wani bata lokaci ba wajen sharara wa saurayin mari a gaban jama'a

A cikin wani faifan bidiyo da ke tashe a dandalin sada zumunta, an ga wata budurwa ta dukusa a gaban saurayinta domin mika masa bukatar su yi aure a gaban jama'a.

Saurayin, wanda ya kasance mai tsananin kunya, ya yi matukar girgiza da abinda budurwarsa. Kazalika, ya nuna alamun nuna kin amincewa da bukatar ta, lamarin da ya kai ga har jama'ar da ke wurin sun fara kyara masa alamun cewa ya amsa bukatar ta.

Duk da nuna alamun kin amincewa da bukatar ta, matar bata daina rokon saurayin ya amince su yi aure ba yayin da take durkushe a kan gwuiwoyinta.

Bayan saurayin ya tirje a kan amsa mata cewa zai aure ta ne, sai budurwar ta tashi cikin bacin rai ta sharara masa mari. Sannan ta fara magana cikin bacin rai yadda ya kunyata ta, ya ki amince wa da bukatar su yi aure duk da sun shafe tsawon shekaru 6 suna soyayya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel