Tsohuwa fitacciyar fim din Indiya ta kashe diyarta budurwa, ta kashe kan ta (Hotuna)

Tsohuwa fitacciyar fim din Indiya ta kashe diyarta budurwa, ta kashe kan ta (Hotuna)

Toshuwar jarumar fina-finan kasar Indiya, Pradnya Parkar, mai shekaru 40 ta kashe diyarta budurwa kafin daga bisani ta kashe kan ta.

Parkar ta kashe matashiyar diyarta ne ta hanyar shake mata wuya a gidansu dake unguwar Kalwa a yankin Gauri Suman, kamar yadda 'yan sanda a Thane suka sanar ranar jama'a da safe.

Tsohuwar jarumar ta bar wasika kafin mutuwar ta inda ta amsa cewa ita ta kashe diyarta, Shruti, mai shekaru 17, daliba a makarantar sakandire dake Thane.

A cikin wasikar, jarumar ta bayyana cewa tana cikin damuwa mai tsanani.

Sakamakon bincike na farko-farko da jami'an 'yan sanda suka sanar ya nuna cewa Parkar ta dade a gida ba tare da samun gayyata domin fito wa a wani shirin fim ba. Kazalika, mijinta ma yana fuskantar kalubale a cikin harkokin kasuwancinsa.

DUBA WANNAN: Tarihin attajirin mai garkuwa da mutanen da ya haddasa rikici tsakanin 'yan sanda da sojoji

Wani babban jami'in dan sanda a ofishin Kalwa, Shekhar Bagde, ya bayyana cewa daga cikin damuwar marigayiyar akwai batun cewa ta gano mijinta na mu'amala da mata a waje.

Parkar ta kashe diyarta da kan ta ne da misalin karfe 8 zuwa 9 na safe lokacin da mijinta ya fita motsa jiki.

Sai da makwabta suka taimaka wa mijin aka balle kofar gidan da marigayiyar ta rufe kafin ta aikata kisan da ta yi.

"Ta bar takardar cewa ita ce ta aika kisan, kuma kar a zargi kowa. Anna muna tunanin cewa matsalolin kudi ne silar damuwar ta," a cewar Badge.

Tsohuwa fitacciyar fim fin Indiya ta kashe diyarta budurwa, ta kashe kan ta (Hotuna)
Parkar da diyarta
Asali: Facebook

Tsohuwa fitacciyar fim fin Indiya ta kashe diyarta budurwa, ta kashe kan ta (Hotuna)
Parkar da diyarta
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel