Yanzu Yanzu: Adam A. Zango ya yi hadarin mota a Nijar

Yanzu Yanzu: Adam A. Zango ya yi hadarin mota a Nijar

Shahararren jarumin Kannywood kuma mawaki, Adam A. Zango ya yi hatsarin mota a kan hanyarsa ta dawowa daga Jamhuriyar Nijar tare da wasu abokansa kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Instagram.

Amma jarumin ya ce babu abinda ya same su sai dai motarsu ce hatsarin ya yi wa illa kamar yadda BBC ta ruwaito

Zango yana yawan yin balaguro musamman lokutan bukukuwa ko shagali kamar na sallah babba da karama saboda gayyatarsa da ake yi domin yin casu.

DUBA WANNAN: Tsohon kwamishinan 'Yan sanda ya fadi wadanda ke daukan nauyin 'yan bindiga a Najeriya

Duk kokarin da BBC tayi don ji ta bakinsa kan lamarin bai yi wu ba kawo yanzu saboda bai amsa wayarsa ba.

Sai dai bayyanai a shafinsa na Instagram sun nuna cewa jarumin ya tafi Niyami, babban binrin Nijar ne don yin wasan sallah.

Galibi dai a kan samu yawaitan hadurra a hanyoyin Najeriya musamman lokutan bukukuwa kamar Sallah, Kirsimeti da bikin sabuwar shekara.

Masu nazarin al'amura su kan daganta hakan da rashin kyawun tituna da kuma tukin ganganci daga bangaren direbobi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: