Asirin Sojan daya kashe Yansanda 3 a Taraba kuma ya tseratar da Wadume ya tonu

Asirin Sojan daya kashe Yansanda 3 a Taraba kuma ya tseratar da Wadume ya tonu

Binciken da rundunar Yansandan Najeriya ta kaddamar ya bankado dadaddiyar alaka tsakanin wani hafsan Soja mai mukamin kyaftin da kasurgumin barawon mutanen nan da ake nema wurjanjan a jahar Taraba, Hamisu Bala Wadume.

Jami’an tsaro bisa umarnin kwamitocin da aka kafa don binciken bahallatsar data biyo bayan harin da Sojoji suka kai ma Yansanda a garin Ibbi na jahar Taraba wanda ya yi sanadiyyar mutuwar Yansanda 3, da tserewar wani barawon mutane, Wadume, sun cigaba da farautar Wadume wurjanjan.

KU KARANTA: Yansanda sun cigaba da farautar Wadume wurjanjan, sun kwace gidajensa da motoci

Yansanda uku da suka mutu sun hada da Inspekta Mark Ediale, Sajan Usman Danazumi, da Dahiru Musa, wanda a yanzu haka an garzaya da gawarwakinsu zuwa babban birnin tarayya Abuja don binciken gawarwakin, sai kuma wasu Yansanda 2 da suka jikkata wanda suma an mayar dasu Abuja don samun kulawa.

Binciken ya gano Kyaftin da Wadume sun yi magana ta wayar salulau har sai 191 a cikin wata daya kacal, daga ranar 9 ga watan Yuli zuwa 6 ga watan Agusta, kamar yadda rahoton Daily Nigerian ya tabbatar.

Wata majiya ta karkashin kasa dake shelkwatar Yansandan Najeriya ta bayyana cewa a yanzu haka shelkwatar Sojojin Najeriya ta kasa ta na binciken wannan kyaftin, tare da wasu Sojoji guda 5 da suka bude ma Yansandan wuta.

Majiyar ta kara da cewa alamu sun nuna Sojan yana taimaka ma Wadume wajen aikata miyagun ayyuka, inda shi kuma yake bashi cin hancin miliyoyin nairori, haka zalika sauran Sojojin 5 sun bayyana cewa kyaftin din ne ya basu umarnin su kai ma motar hari a kan cewa barayi sun yi garkuwa da Wadume.

A hannu guda kuma hukumar Yansandan Najeriya ta tabbatar da alaka tsakanin Wadume da wannan Soja, inda tace bincikenta ya nuna Wadume na biyan Sojan albashi mai tsoka, yayin da shi kuma yake daure masa gindi wajen satar mutane tare da garkuwa dasu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel