Ana zanga-zangar neman sakin El-zakzaky a Indiya

Ana zanga-zangar neman sakin El-zakzaky a Indiya

Rahotanni sun bayyana cewa, wasu 'yan kasar Indiya sun yi dandazo a gaban ofishin jakandancin Najeriya da ke kasar inda suke gudanar da zanga-zanga ta yin kira tare da nema sakin jagoran kungiyar IMN wadda aka fi sani da shi'a, Sheikh Ibrahim El-zakzaky.

Ana iya tuna cewa, a ranar da ta gabata ne jagoran kungiyar IMN (Islamic Movement of Nigeria) tare da mai dakinsa, Zeenatu, suka sauka a birnin New Delhi na kasar Indiya domin neman lafiya bayan da babbar kotun jihar Kaduna ta ba su izini.

Gabanin haka, jagoran mabiya akidar shi'a tare da mai dakinsa, sun kasance tsare a hannun jami'an hukumar 'yan sandan farin kaya ta DSS tun kimanin shekaru fiye da uku da suka gabata.

Sai dai a yanzu kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, wasu 'yan kasar Indiya sun yi kira na neman a saki El-zakzaky yayin da suka yi dandazo a gaban ofishin jakadancin Najeriya wajen gudanar da zanga-zanga dauke da tutoci masu rubutun neman cikar kudirin su.

KARANTA KUMA: Buhari ya kaddamar da sabon titi na N3.3bn a Katsina

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, likitocin kasar Indiya tuni suka dukufa wajen fara duban lafiyar madugun kungiyar IMN tare da mai dakin sa tun bayan isar su a ranar Talatar da gabata.

A wani rahoton mai nasaba da wannan, Sheikh Muhammad Yakoob, dan uwa ga jagoran 'yan darikar shi'a ne Najeriya, ya ce kasar Iran ce tayi amfani da wajen sauya tunani tare da jan ra'ayin dan uwansa a akan akidar shi'a da a cewarsa ta munana.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel