Tafiya kasar Indiya: El-zakzaky ya ki hawa jirgin fadar shugaban kasa

Tafiya kasar Indiya: El-zakzaky ya ki hawa jirgin fadar shugaban kasa

Bayan cin sarka ta fiye da tsawon shekaru uku, shugaban kungiyar IMN wadda aka fi sani da shi'a, Sheikh Ibrahim El-zakzaky da kuma matarsa, Zeenatu, a ranar Litinin sun bar Najeriya zuwa kasar Indiya wajen neman lafiya.

Jagoran mabiya akidar shi'a tare da mai dakin sa sun tashi ne daga filin jirgin saman kasa da kasa na Nnamdi Azikwe dake birnin Abuja zuwa kasar Indiya domin neman lafiya.

Wannan lamari ya biyo bayan hukuncin da babbar kotun Kaduna bisa jagoranci Alkali Darius Khobo ta zartar, na bai wa El-zakzaky tare da mai dakinsa izinin tafiya kasar Indiya wajen neman lafiya kamar yadda suka bukata.

Binciken manema labarai ya tabbatar da cewa, El-zakzaky tare da mai dakinsa sun yi watsi da tayin fadar shugaban kasa na amfani da daya daga cikin jiragenta wajen aiwatar da wannan baluguro, inda suka yanke shawarar bin jirgin 'yan kasuwa.

Jagoran darikar shi'a na Najeriya ya tafi kasar Indiya cikin jirgin kamfanin Emirates a ranar Litinin kamar yadda kakakin kungiyar IMN, Ibrahim Musa ya bayar da tabbaci a wata hira da manema labarai ta hanyar wayar tarho.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Buhari ya karbi gaisuwar sallah ta manyan Najeriya a gidansa na Daura

A wani rahoto mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, kungiyar IMN ta ce abinda ta dade tana gwagwarmaya ya tabbata biyo bayan ficewar jagoranta El-zakzaky neman magani zuwa Indiya. Kungiyar ta ce ta jingine duk wata zanga-zanga a sakamakon cikar burinta.

Kazalika jaridar ta ruwaito cewa, da misalin karfe 4.00 na safiyar ranar Litinin 12 ga watan Agustan 2019, jirgin Emirate mai lamba EK2614 wanda ya yi dakon jami'an tsaro, El-zakzaky tare da Zeenatu, ya yada zango a kasar Dubai gabanin ci gaba da balaguro zuwa kasar Indiya.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel