Matar gwamna El-Rufai ta yi rabon abincin Sallah ga marasa lafiya (Hotuna)

Matar gwamna El-Rufai ta yi rabon abincin Sallah ga marasa lafiya (Hotuna)

Matar gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, Hajiya Ummi Garba El-Rufai ta kai ziyara zuwa wasu manyan asibitocin jahar Kaduna guda uku dake cikin garin Kaduna inda kai ma marasa lafiya dauki.

Ummi ta kai wannan ziyara ne a ranar Litinin, 12 ga watan Agusta domin ta dandana marasa lafiya dake jinya a asibitocin dandanon shagulgulan babbar Sallah sakamakon basa iya fita saboda lalurar dake damunsu.

KU KARANTA: Tambuwal ya raba ‘Goron Sallah’ naira miliyan 70 ga alhazai 3,496

Matar gwamna El-Rufai ta yi rabon abincin Sallah ga marasa lafiya (Hotuna)
Hajiya Ummi
Asali: Twitter

Legit.ng ta ruwaito Hajiya Ummi ta fara ziyarar ne da asibitin Barau Dikko, daga nan ta zuwa asibitin Yusuf Dantsoho wanda ake kira asibitin Dutse, sai kuma ta gangara babban asibitin Kawo.

A yayin ziyarar, Hajiya Ummi, wanda it ace matar Gwamna El-Rufai ta uku ta raba marasa lafiya kullin abinci, da kuma kayan shaye shaye na ruwa, sa’annan ta tattaunawa dasu tare da share musu hawaye.

Matar gwamna El-Rufai ta yi rabon abincin Sallah ga marasa lafiya (Hotuna)
Hajiya Ummi
Asali: Twitter

A wani labarin kuma, G=gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya samu wata babbar sarauta daga masarautar Kagarko dake karkashin jagorancin Sarkin Kagarko, Alhaji Sa’ad Abubakar.

Mai martaba Sarki ya nada gwamnan sarautar ‘Sadaukin Kagarko’, kuma a ranar Lahadi, 11 ga watan Agusta aka yi bikin nadinsa sarautar a fadar mai martaba Sarki bayan kammal sallar Idi.

Sarki Sa’ad ya bayyana cewa masarautar ta ga da cewa nada Gwamna El-Rufai sarautar ne sakamakon muhimmiyar rawar da yake takawa wajen kawo cigaba mai daurewa a masarautar dama jahar gaba daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel