Dakarun rundunar Sojan sama sun tafka ma Boko Haram mummunan asara

Dakarun rundunar Sojan sama sun tafka ma Boko Haram mummunan asara

Dakarun rundunar Sojan sama dake yaki da mayakan Boko Haram a yankin Arewa maso gabashin Najeriya sun samu wata gagarumar nasara a kan mayakan ta’addanci a wata samame da suka kai musu ta sama.

Sojojin sun yi amfani da sabbin jiragen yakin da gwamnatin Najeriya ta sayo musu ne wajen zazzaga ma yan ta’addan ruwan bama bamai, inda a dalilin haka suka kassara wani cibiyar tsare tsaren yaki na Boko Haram yankin Izza cikin dajin Sambisan jahar Borno.

KU KARANTA: Miyagu yan bindiga sun kaddamar da farmaki a wata jami’ar Najeriya

Kaakakin rundunar, Ibikunle Daramola ya bayyana haka a ranar Litinin, 12 ga watan Agusta a babban birnin tarayya Abuja, inda yace baya ga lalata cibiyar tsare tsare, jiragen yakin sun kashe adadin Boko Haram da dama.

Kaakakin yace kafin su kaddamar da wannan samame, sai da suka gudanar da binciken kwakwaf domin tabbatar da inda zasu sauke bamabaman ta hanyar amfani da na’aurorin kimiyya daban daban.

“Bayan sun tabbatar da kasantuwar mayakan Boko Haram da dama a cikin wannan cibiya na tsare tsaren yaki, sai muka aika da jiragen yaki guda uku kirar Alpha Jet zuwa wajen, nan da nan kuma tafka musu mummunan asara.” Inji shi.

Daga karshe kaakaki Daramola yace ba za su yi kasa a gwiwa wajen cigaba da kakkabe ragowa mayakan Boko Haram daga yankin Arewa masu gabashin Najeriya ba, don haka suke neman gudunmuwar al’ummar dake zaune a yankin don cima burinsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel