Rashford ya haddasawa Chelsea mafi munin shan kashi tun 1965 bayan 4-0

Rashford ya haddasawa Chelsea mafi munin shan kashi tun 1965 bayan 4-0

Yayin da a kawo dawo buga kwallon kafa a kasar Ingila, kungiyar Manchester United ta yi wa Takwararta Chelsea raga-raga a karawar da su kayi dazu a wasan farkonsu na gasar EPL na bana.

Chelsea ta sha kashi ne da ci har hudu da nema a wasan dazu da yamma. ‘Dan wasa Marcus Rashford shi ne ya jefa kwallaye biyu a ragar Chelsea, Anthony Martial kuma ya zura kwallo guda.

Marcus Rashford ya fito da kan shi ne a daidai lokacin da jama’a ke tunanin ko koci Ole Gunner Solskjaer zai kai Man Utd ga nasara a kakar bana bayan ya saida ‘dan wasan gaba Romelu Lukaku.

Sabon ‘dan wasan David James ya leka ragar ta Chelsea wanda sabon Kocinta Frank Lampard ya ke kokarin gane bakin zaren a tsohon kulob din na sa wanda ta ke kukar rabuwa da Tauraro Eden Hazard.

KU KARANTA: Barcelona ta fara wasanni ba tare da babban 'Dan kwallonta ba

Wannan ne mafi munin kashin da Chelsea ta sha hannun Manchester United a cikin shekaru 54. Tarihi ya nuna cewa rabon da manyan kulob din su yi arangama a farkon kaka tun a shekarar 2004.

Sabon Kocin Chelsea wanda ya yi amfani da irinsu 'dan wasa Mason Mount da Christian Pulisic ya bayyana cewa bai kamata a dika masu kwallaye har hudu ba. Lampard ya ce sun tabuka abin kirki.

‘Dan wasan bayan da Manchester United ta saya Harry Maguire, ya buga wannan wasa inda ya nunawa Duniya kwarewarsa. An saye Maguire ne a kan kudi fam miliyan £85 a kakar kasuwar bana.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel