Zaben kananan hukumomi: PDP ta lashe dukkanin kujeru 8 a jihar Bayelsa

Zaben kananan hukumomi: PDP ta lashe dukkanin kujeru 8 a jihar Bayelsa

Mun samu cewa, babbar jam'iyyar hammaya a Najeriya PDP, ta lashe dukkanin kujeru takwas na kananan hukumomi da jihar Bayelsa ta kunsa yayin da aka kammala zaben kananan hukumomin jihar wanda hukumar zabe reshen jihar ta gudanar a ranar Asabar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito, jam'iyyar APC ba ta shiga zaben ba na kananan hukumomin jihar Bayelsa a sakamakon wata 'yar tangarda gami da tufka da warwara da ta fuskanta kamar yadda ta yi ikirari.

Baturen zabe Mista Frank Ebikumor a ranar Lahadi cikin birin Yenagoa, ya bayar da sanarwar cewa, Mr Dengiye Ubarugu na jam'iyyar PDP, ya lashe zaben karamar hukumar Kolokuma/Opokuma da kuri'u 42, 539, yayin da lallasa abokin adawarsa na jam'iyyar ADC mai kuri'u 1,031 kacal.

A Ijaw ta Kudu kuma, baturen zaben Dr Nwiwu Johnson, ya bayar da sanarwar cewa, Mr Nigeria Kia na jam'iyya PDP, ya lashe zabensa da kuri'u 107,150 yayin da jam'iyyar AD ta samu kuri'u 2,489 kacal.

A karamar hukumar Ekeremor kuma, baturen zaben Dr Victor Ayibatonye, ya sanar da Cif Perekeme Petula na jam'iyyar PDP a matsayin gwarzo bayan samun kuri'u 62,529 yayin da babu ko jam'iyya daya da ta fito adawa.

Haka kuma karamar hukumar Sagbama da ta kasance mahaifar gwamnan Bayelsa, Seriake Dickson, dan takarar jam'iyyar PDP, Mr Alah Embeleakpo, ya lashe zaben da kuri'u 98,468 yayin da nan ma babu wata jam'iyyar da ta fito adawa kamar yadda baturen zabe Dr ThankGod Apere ya bayyana.

Baturen zabe na karamar hukumar Brass, Mr Timothy Ogiaba, ya sanar da Victor Isaiah na jam'iyyar PDP, a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri'u 28,667, yayin da jam'iyyar LP ta samu kuri'u 2,948 kacal.

A karamar hukumar Ogbia, Mista Turner Ebinyo na jam'iyyar PDP, shi ne wanda ya lashe zaben da kuri'u 17,661 yayin da jam'iyyar ADC ta samu kuri'u 1,071 kacal kamar yadda baturen zabe Mista Ebiye Ogoli ya bayyana.

KARANTA KUMA: Sanata Ahmed Lawan ya taya musulmai murnar babbar Sallah

Baturen zabe na karamar hukumar Yenagoa, Dakta Good-head Abraham, ya sanar da Uroupaye Nimizoua na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri'u 98,831 yayin da dan takara na jam'iyyar ADC, Lawrence Kwokwo na jam'iyyar ADC ya samu kuri'u 636 kacal.

Da yake zayyana jawabansa, shugaban hukumar zabe na jihar Bayelsa, Dr. Remember Ogbe, ya bayyana farin cikinsa dangane da yadda zaben kananan hukumomin jihar ya gudana cikin lumana da kwanciyar hankali.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng