Sukar Zakzaky: Kungiyar IMN ta mayarwa Sheikh Yakoob martani mai zafi

Sukar Zakzaky: Kungiyar IMN ta mayarwa Sheikh Yakoob martani mai zafi

Sakataren bangaren Ilimi na kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN), Abdullahi Musa ya yi ikirarin cewa Sheikh Mohammed Yakoob, yayan Sheikh Ibrahim El-Zakzaky yana yi wa shigaban na Shi'a bakin ciki ne.

Musa ya bayyana hakan ne yayin da ya ke mayarwa Yakoob da martani kan sukar shugabansu da ya yi na cewa Iran tayi amfani da kudi ne ta janyo ra'ayin shugaban na IMN da yanzu ya ke tsare kuma ya ce shine ya janyo duk fitinun da suka same shi.

A hirar da ya yi da The Cable a ranar Asabar, Musa ya ce ya kamata yayan El-Zakzaky ya ji kunyan furta irin magangunan da ya fadi.

DUBA WANNAN: Abun kunya: Dan majalisar PDP ya yi wa wata mata zigidir a bainar jama'a

A yayin da ya ke karyata zancen da yayan Zakzaky ya fadi na cewa kudi ne akayi amfani da shi don janyo hankalin Zakzaky, ya ce babu wani adadin kudin da za a iya bawa mutum ya salwantar da rayuwarsa.

"Maganganu marasa tushe ne kawai tsohon ya furta. Suna kishi ne kawai don yana da miliyoyin magoya baya," inji shi.

"Saboda Allah, nawa Tehran za ta bawa mutum don ya sadaukar da rayuwansa? An kashe masa yara, an kone kadarorinsa.

"A addinin kirista, akwai 'yan darikar Katolika da ke da alaka da Rome, suma za a ce suna yin addinin kiristanci ne saboda wani na daukan nauyin su?"

A ranar Litinin, wata babban kotu a Kaduna ta bawa El-Zakzaky da mai dakinsa izinin zuwa neman magani a kasar India. Shugaban na IMN da mai dakinsa sun nemi izinin tafiya kasar wajen a dalilin rashin lafiya da suka fama da shi.

Sai dai gwamnatin jihar Kaduna ta sake gindawa wa El-Zakzaky wasu sharruda kafin ya tafi kasar ta India neman maganin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel