Na sha zagi kan mayar da naira miliyan 15 da na tsinta – Kofur Umar

Na sha zagi kan mayar da naira miliyan 15 da na tsinta – Kofur Umar

Kofur Bashir Umar, jami’in sojan sama na Najeriya, wanda ya tsinci kudi kimanin naira miliyan 15 da wani bawan Allah ya yar a filin jirgin sama na Aminu Kano ya bayyana irin sukar da ya sha akan mayar wa mai kudin da abinsa.

A cewar Bashir ya sha zagi sosai a wajen wasu mutane, inda har wasu suka kira shi da matsiyaci saboda aikin alkhairi da yayi na mayar da kudin.

Bashir yace wadansu mutane ma har cewa suka yi shi da yin arziki a rayuwarsa sunyi hannun riga.

Shafin jaridar Aminiya ta ruwaito inda Bashir ke cewa: “Na sha zagi daga wadansu mutane, domin kuwa wadansu har ce mini suka yi ni matsiyaci ne, har abada ba zan yi arziki ba a rayuwata.”

Sai dai kuma yace duk da haka wasu sun yaba masa sosai, inda yace “Amma wadansu kuma sun yaba mini, don haka na samu maganganu iri daban-daban daga mutane dangane da wannan al’amari. Sai dai kuma ba na nadamar wannan mataki da na dauka, maimakon nadama ma, farin ciki na samu a lokacin da na mayar da kudin ga mai su.”

Ya kuma shawarci jama’a da su yi kokarin mmayar da duk wani abu da suka tsinta zuwa ga mamallakin abun domin a cewarsa “Ya kamata mutum ya sani cewa koda daidai da Naira biyar ka dauka daga kayan wani, akwai hukunci na nan yana jiranka a Ranar Lahira. Kuma lallai sai ka biya mai hakki hakkinsa.”

KU KARANTA KUMA: Yarinya yar shekara 6 ta nuna bajinta inda ta sha gwagwarmaya da wanda yayi garkuwa da ita, sannan ta gane shi

Ku sani cewa kafin faruwar wannan lamari, Bashir kurtu ne, amma sanadiyyar wannan abin kirki da ya yi aka kara masa girma har rubi biyu, daga kurtu zuwa Kofur. Baya ga wannan karin girma, Babban Hafsan Sojan Sama, Iya Mashal Sidikue Abubakar da kansa ya daura masa igiyar mukaminsa, a wani kwarya-kwaryan biki da aka gudanar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel