'Yar gidan mataimakin shugaban kasa Kiki Osinbajo ta yi wata muhimmiyar magana game da rayuwar

'Yar gidan mataimakin shugaban kasa Kiki Osinbajo ta yi wata muhimmiyar magana game da rayuwar

- Ta bayyana cewa tayi aiki tukuru domin ganin ta zama wata a rayuwa duku kuwa da cewa ga irin gidan da ta fito

- Ta bayyana irin kalubale da ta fuskanta da kuma irin mutanen da take mu'amala dasu a rayuwarta

- Ta ce ta san ta fito daga gida na jin dadi amma hakan bai hana ta neman na kanta ba

'Yar gidan mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo kuma 'yar kasuwa mai shekaru 26, Kiki Osinbajo ta wallafa wata magana a shafinta na Instagram akan yadda ta tafiyar da kasuwancin ta, sannan kuma da shirin da take yi na cigaba da harkar kasuwancinta.

Kiki ta bayyana cewa duk da an haifeta cikin jin dadi, amma babu wanda zai ce bata aiki tukuru domin ganin ta zama wata a rayuwa.

KU KARANTA: Allah ya kyauta: An rufe hanyar Kaduna zuwa Abuja bayan wani dan sanda ya harbe wani direban mota har lahira

Da take magana akan kasuwancin ta, Kiki wacce ta kammala jami'ar Aston ta bayyana yadda take cinyi kowacce rana ta neman mafita ga rayuwarta.

Sannan kuma tayi magana akan, abubuwan da suke bata tsoro, kalubalen da take samu, da kuma yadda take mu'ammala da 'yan bani na iya, da kuma mutanen da suke ganin ba sai tayi aiki ba a rayuwarta.

"Shekaru kadan da suka gabata na yanke shawarar fara kasuwanci na, yanzu kuma na ga yadda kasuwancina ya kafu," in ji ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel