Kogi 2019: Kotu ta dakatar da APC daga amfani da daliget
Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umurnin dakatar da shirin amfani da daleget wurin fitar da 'yan takara yayin zaben cikin gida na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kogi har sai lokacin da aka yanke hukunci.
Alkalin kotun, Justice Taiwo ne ya bayar da wannan umurnin a ranar Juma'a yayin yayin sauraron karar da wasu 'yan jam'iyyar magoya bayan Hadd Ametuo suka shigar da suka hada da Destiny Eneojoh Aromeh, Isah Abubakar, Noah Aku da Mrs. Joy Onu.
Justice Taiwo ya kuma bayar da umurnin sauraron shari'ar cikin gaggawa duba da cewa a ranar 29 ga watan Augustan 2019 ne za a gudanar da zaben fidda gwanin na kogi gabanin zaben gwamna da za a yi a jihar.
DUBA WANNAN: Matakan da zan dauka kan rikicin Majalisun Bauchi da Edo - Buhari
Alkalin ya bukaci masu shigar da karar su gabatarwa kotu dukkan takardun da ake bukata kuma ya ce za a saurari karar a ranar 19 ga watan Augusta.
Wadanda suka shigar da karar sun sun roki kotu ta bayar da umurnin haramtawa wadanda akayi karar da mukarrabansa yin amfani da daliget yayin zaben cikin gida na jam'iyyar domin fitar da 'yan takarar da za su wakilci jam'iyyar a zaben gwamnan da za ayi a Kogi.
A ranar Alhamis ne alkalin kotun ya saurari bangarorin biyu kan batun salon da za ayi amfani da shi wurin zaben cikin gidan amma ya bayar da hukuncinsa a yau Juma'a.
Muhimmin abinda karar da aka shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/833/2019 shine neman kotun ta hana Kwamitin Gudanarwa na Jam'iyyar amfani da dakliget wurin yin zaben fidda gwani na jam'iyyar da za ayi ranar 29 ga watan Augusta gabanin zaben gwamnan jihar da za ayi a ranar 16 ga Nuwamban 2019.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng