Abun kunya: Dan majalisar PDP ya yi wa wata mata zigidir a bainar jama'a

Abun kunya: Dan majalisar PDP ya yi wa wata mata zigidir a bainar jama'a

An gurfanar da wani dan majalisar jihar Akwa Ibom a gaban babban kotun da ke Uyo bisa zarginsa da yi wa wata mata duka da yi mata tsirara a bainar jama'a.

Wanda ake zargin mai suna Uduak Nseobot kansila ne a karamar hukumar Ibiona da ke jihar ta Akwa Ibom.

Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta gurfanar da Mr Nseobot da mai dakinsa Aniedi a ranar 11 ga watan Yuli inda ake tuhumarsa da sace wata Iniubong Essien inda suka mata duka sannan suka yi mata tsirara a bainar jama'a bisa zargin ta da sace musu kudi.

Sun ce ta sace kudin ne a wurin bikin su yayin da mutane ke musu 'liki' kamar yadda aka saba a wasu wurare idan ana bikin aure a Najeriya.

Abun kunya: Dan majalisar PDP ya yi wa wata mata zigidir a bainar jama'a
Abun kunya: Dan majalisar PDP ya yi wa wata mata zigidir a bainar jama'a
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Matakan da zan dauka kan rikicin Majalisun Bauchi da Edo - Buhari

Sai dai Ms Essien wace kawar mai dakin kansilar ne na tsawon shekaru 10 ta musanta cewar ta saci kudi a wurin bikin.

Ta shaidawa Premium Times cewa ta taimaka wa iyalan kansilan wurin girki da rabon abinci yayin bikin amma ba ita bane ta taya su kwashe kudaden da aka lika musu a wurin bikin.

An ce kansilar da matarsa da abokansu sun sace Ms Essien daga gidanta da safe a Nuwamban 2018 suka tafi da ita kauyen Ibiono mai nisan kilomita 27 daga Uyo.

Daga nan suka kai ta wani dakin taro a kauyen misalin karfe 10 na safe.

Ms Essien ta ce, "Sun tube min kaya na da breziya da dan kamfai bayan sun nakada min duka.

"Akwai mutane cikin dakin taron da aka kai ni, ina tsamanin ya tara su ne ya fada musu cewa zai kawo barauniya saboda suyi mata duka.

"Sun daura igiya a kugu na suka ce wai dole sai nayi rawa tsirara yayin da matar kansilar da kawayenta su kayi da dauka na hoto da bidiyo da wayoyinsu na salula bayan an gama duka na."

Lauya mai kare wanda akayi kara, Mfon Ben ya shaidawa kotu cewa wanda ya ke karewa ya shigar da karar kallubalantar inganci karar da aka shigar a kansa.

Alkalin kotun ya amince da bukatar da lauyan kansilar ya shigar na jinkirta amsa laifinsa har sai an saurari bukatar da ya shigar kan kallubalantar karar.

Kotu ta dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 14 ga watan Oktoba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel