Tirkashi: Wani dan majalisa ya takarkare ya banka tusa a dakin majalisa da ta sanya kowa ficewa daga dakin

Tirkashi: Wani dan majalisa ya takarkare ya banka tusa a dakin majalisa da ta sanya kowa ficewa daga dakin

- Wani abin kunya da ya faru a kasar Kenya ya jawo kace-nace a dakin majalisar kasar na tsawon mintuna goma

- Abin da ya faru kuwa shine, yadda wani dan majalisa ya takarkare ya banka tusa a dakin majalisar, wacce tayi sanadiyyar kowa ya fara zargin kowa

- Wannan tusa ta sanya kakakin majalisar ya bayyana cewa a tsaya da zaman majalisar na tsawon wani lokaci kafin warin ya fita

Wani dan majalisa da ya banka tusa a dakin majalisa ya yi sanadiyyar da ya sanya dole aka rufe dakin majalisar kasa Kenya, yayin da 'yan majalisar suka fara zargin junansu akan warin tusar.

Dan majalisar da ba a san ko waye bane, ya banka tusar a dakin majalisar Homa Bay a ranar Larabar nan da ta gabata, bayan dan majalisa daya daga cikinsu ya zargi dan uwansa da yin tusar.

A yadda rahoto jaridar DailyMail ya nuna, dan majalisar da ake zargin ya karyata zargin da ake yi masa, inda ya bayyana cewa babu yadda za ayi yayi irin wannan abin kunyar a gaban abokanan aikinshi.

KU KARANTA: Labarin wani mutumi da ya yi shekara 40 ba tare da yayi aski ba

Cikin gaggawa kakakin majalisar ya bukaci a kawo turare wanda zai kawo saukin warin tusar.

Wannan tusa dai ta yi sanadiyyar da ya sanya aka daga taron majalisar na tsawon minti goma, yayin da kakakin majalisar ya bayyana cewa ba zai yiwu su cigaba da zama a cikin wannan wari ba.

Idan ba a manta ba a cikin satin nan ne aka kori wata 'yar majalisa ta kasar ta Kenya daga dakin majalisar saboda ta shiga da jaririyarta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel