Kalli wani Alhaji yana dawafi dauke da mahaifiyarsa a wuyarsa

Kalli wani Alhaji yana dawafi dauke da mahaifiyarsa a wuyarsa

Kyautata ma iyaye babban lamari ne a addinin Musulunci kamar yadda wani mutumi da ya tafi kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajji tare da mahaifiyarsa ya dabbaka.

Legit.ng ta ruwaito wannan mutumi da ba’a bayyana sunansa ba ya ciccibi mahaifiyarsa dattijuwa a wuyarsa, inda ya dinga zagayen Ka’aba dakin Allah da ita, ma’ana dai ya gudanar da dawafi dauke da mahaifiyarsa a wuyarsa.

KU KARANTA: Hukumar aikin Hajji ta karrama Limamin daya ceci Kiristocin Berom 300, a Saudiya

Wannan bidiyo daya tuni ya watsu a kafar sadarwar zamani ta Facebook ya tabbatar da soyayyar dake tsakanin Da da Uwa, kuma bidiyon ya burge jama’a da dama tare da baiwa miliyoyin mutane sha’awa, inda aka dinga madalla da wannan bawan Allah.

A wani labarin kuma, Hukumar aikin Hajji ta Najeriya, NAHCON ta karrama wasu Musulmai yan Najeriya guda biyu da suka nuna kyawawan halaye abin koyi, a yayin aikin Hajji na bana.

Legit.ng ta ruwaito wadannan mutane biyu sun hada ne da Imam Abubakar Abdullahi, limamin wani Masallaci dake jahar Filato wanda ya ceci wasu kiristoci yan kabilar Berom fiye da 300 daga harin yan bindiga, da kuma Kofur Bashir Umar, Sojan daya tsinci N15,000,000 kuma ya mayar.

Hukumar NAHCON ta karrama Imam Abubakar ne ta hanyar sanyashi cikin tawagar Malaman Hajji ta kasa da zasu gudanar da wa’azuzzuka da tunatarwa ga mahajjatan Najeriya a yayin aikin Hajji.

Haka zalika hukumar ta karrama Kofur Bashir Umar ta hanyar sanyashi daga cikin jami’an kwamitin tsaro na hukumar da zasu kula da tsaron alhazan Najeriya da dukiyoyinsu a yayin zamansu a kasar Saudiyya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel