Malamin addini ya matsa layar zana bayan ya dirka wa wata marainiya ciki
Wani malamin Coci a yankin Binga na kasar Zimbabwe ya cika wandonsa da iska bayan ya dirka wa wata matashiyar marainiya, mai shekaru 19, ciki yayin da aka tura shi cocin bayan kammala karatu a wata makarantar karatun Injila (Bible).
Jaridar 'The Cgronicle' ta rawaito cewa faston da aka fi kira da 'Mushayavanhu' ya yi wa matashiyar, da wasu bayin Allah suka dauka domin jin kan ta, ciki ta hanyar amfani da matsayinsa na daya daga cikin limaman Cocin.
Mai rikon matashiyar ya shaida wa manema labarai cewa Malamin ya cika wandonsa da iska tun bayan da batun juna biyun ya fito fili.
Sai dai, Fasto Mushayavanhu ya dauki alhakin yi wa matashiyar ciki a yayin da masu rikon matashiyar suka kai kukansu ga babban faston Cocin.
DUBA WANNAN: Wata budurwa ta rataye kan ta saboda ta yi cikin shege
"A watan Janairu aka kawo Fasto Mushayavanhu garin Binga, kuma tun da aka kawo shi yake zaune a wani bangare na gidan mu da mahaifiyata ta bawa Cocin haya. A watan Afrilu ne kuma muka gano cewa yarinyar na dauke da juna biyu," a cewar daya daga cikin masu rikon marainiya.
Da aka tuntubi Ndlovu, babban faston Cocin, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana cewa su ma yanzu haka suna neman Fasto Mushavanyahu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng