Allah ya kyauta: 'Yan Bindiga sun hari gidan Sarki a jihar Sokoto, sun kashe dogari sun kuma yi awon gaba da kanin Sarkin

Allah ya kyauta: 'Yan Bindiga sun hari gidan Sarki a jihar Sokoto, sun kashe dogari sun kuma yi awon gaba da kanin Sarkin

- A wani hari da wasu 'yan bindiga suka kai wani kauye dake cikin jihar Sokoto, sun kashe wani dogarin Sarkin garin

- Sannan kuma sunyi awon gaba da kanin mai garin, bayan sun yiwa matar mai garin dukan tsiya

- 'Yan sanda dai sun bayyana nasarar kama daya daga cikin masu laifin, inda suka same shi da wayar matar mai garin a hannunshi

Wani hari da 'yan bindiga suka kai wani gidan Sarki a jihar Sokoto, sun kashe dogarin Sarkin guda daya sannan kuma sunyi awon gaba da dan uwan Sarkin.

Rundunar 'yan sanda ta jihar Sokoto ta bayyana cewa ta kama wani mai suna Maude Salisu, wanda ta kama da hannu a wannan lamari, sannan kuma ta ce sunan dogarin da aka kashe Usman Muhammadu. Kwamishinan 'yan sandan jihar Ibrahim Kaoje shine ya bayyana manema labarai cewa:

"'Yan bindiga kimanin su bakwai sun kai hari gidaan mai garin kauyen Gidan Bubu dake cikin karamar hukumar Wamakko a jihar Sokoto, Alhaji Muhammadu Gidado, inda suka dinga harbin kan mai uwa da wabi.

KU KARANTA: Tashin hankali: Saurayi da budurwa sun mutu bayan sun fado daga kan gada lokacin da suke rungume-rungume da sunbatar juna

"Sunyi garkuwa da Alhaji Sani Ardo, wanda yake kanine ga mai mai garin, sannan sun yiwa matar mai garin mai suna Hauwa'u Sani dukan tsiya, sannan suka kwace wayarta."

Kwamishinan ya bayyana cewa dan uwan mai garin da aka sace an sako shi bayan an biya 'yan bindigar kudin fansa naira miliyan uku.

"A lokacin da muke gabatar da bincike mun kama wani mai suna Maude Salisu, inda muka same shi da wayar matar mai garin da kuma kudi naira dubu dari hudu da sha bakwai da talatin (N417,030), inda muke zargin kason da ya samu kenan bayan sun raba kudin fansar," in ji Kaoje.

A karshe Maude ya amsa laifinsa, inda yanzu haka kuma yake taimakawa jami'an tsaro wajen cafke masu laifin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel