Toh fah: Jerin jihohi 15 da za su fuskanci matsananciyar ambaliyar ruwa

Toh fah: Jerin jihohi 15 da za su fuskanci matsananciyar ambaliyar ruwa

Hukumar da ke kula da harkokin ruwa ta Najeriya wato Nigeria Hydrological Services Agency (NIHSA), ta ja hankalin jihohin kasar, inda ta bukaci da su sanya ran fuskantar ambaliyar ruwa sosai a lokacin damuna.

Hukumar ta mika gargadin ne kai tsaye ga wasu jihohi 15 da suka hada da Niger, Lagos, Edo, Imo, Abia, Jigawa, Adamawa, Delta, Rivers, Cross Rivers, Oyo, Enugu, Kebbi, Nasarawa, Bauchi da kuma babbar birnin tarayya Abuja.

Da yake Magana a taron manema labarai a jiya Laraba, 7 ga watan Agusta a Abuja, Darakta Janar na hukumar, Injiniya Clement Nze, yace akwai yiwuwar cewa jihohin tarayyar kasar 36 ciki harda birnin tarayya za su fuskanci ambaliyar ruwa a matakai daban-daban a wannan shekarar.

Nze ya ce ambaliyar za ta ci gaba da aukuwa ba kama hannun yaro a watan gobe a sanadiyar cika da batsewar kogin Niger da Benue.

Ya kuma bayyana cewa hukumar ta sanya ido sosai akan lamuran ambaliyar ruwa da ke faruwa a fadin kasar kamar yadda yayi sanadiyar rasa rayuka da dukiyoyi.

KU KARANTA KUMA: Tashin hankali: Saurayi da budurwa sun mutu bayan sun fado daga kan gada lokacin da suke rungume-rungume da sunbatar juna

Nze yayi kira ga cewar akwai bukatar yin tsarin haka manyan magudanar ruwa, da kuma guje ma gida gidaje a wuwaren da ruwa ke gudana da kuma gina wuraren kula da ambaliar ruwa a kasar da makwabta.

Yace amaliyar ruwa na iya zama annoba idan babu abubuwan da ake bukata domin magance shi a kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel