Babbar Sallah: Za mu shirya wasan 'sharo' a Zamfara - Gwamna Matawalle

Babbar Sallah: Za mu shirya wasan 'sharo' a Zamfara - Gwamna Matawalle

- Gwamnatin Jihar Zamfara za ta shirya wasan sharo a garin Gusau da sauran kananan hukumomin da ke jihar

- Gwamna Matawalle ya ce an tsara yin wasan sharon ne na fulani yayin bikin salla domin kara dankon zumunci tsakanin hausawa da fulani a jihar

- Gwamnan ya ce yana fatar cudanya mai kyau tsakanin bangarorin biyu zai taimaka wurin ganin an yafe wa juna abubuwan da suka faru a baya

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya ce gwamnatinsa za ta dauki dauyin shirya bikin Sharo na Fulani da aka fi sani da shadi a birnin Gusau da kuma sauran kananan hukumomin jihar yayin bikin sallah babba.

Sanarwar ta mai taimakawa gwamnan na musamman kan wayar da kan mutane, Zailani Bappa ya fitar a ranar Laraba ta ce gwamnatin za ta shirya bikin sharon ne domin inganta sulhun da ake yi a jihar a halin yanzu.

DUBA WANNAN: 2019: APC za ta iya lallasa PDP a zaben gwamnan Bayelsa - Goodluck Jonathan

Sanarwar ta ce "Wannan zai taimaka mutane wurin kara dankon zumunci tsakanin Fulani da sauran al'ummar jihar a yanzu da ake kokarin kawo karshen rikicin 'yan bindiga a jihar."

"Ana sa ran Fulani da Hausawa za su hallarci wasu bukukuwa da za a yi a karshen mako domin murnar sallah babba ciki har da wasan sharo na Fulani."

Ya ce sulhun da ake yi a yanzu ya sanya Fulani sun fahimci cewa gwamnati mai ci yanzu da gaske ta keyi duba da cewa ta cika alkawurran da ta dauka kawo yanzu.

"An shirya wannan bikin ne domin dukkan bangarorin biyu su yafe wa juna abinda ya faru a baya a jihar Zamfara," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel